Hajjin 2025: Gwamnatin Tarayya ta zaɓi kamfanonin jirage huɗu domin jigilar maniyyata

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta amince da kamfanonin jiragen sama guda huɗu domin jigilar maniyyata Hajjin bana.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) Farfesa Abdullahi Usman ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce an zaɓi kamfanoni huɗu ne daga cikin guda 11 da suka nuna sha’awar aikin jigilar maniyyatan.

Ya ce, kamfanonin huɗu su ne: Air Peace Ltd, da wani kamfanin ƙasar Saudiya mai suna Fly-Nas da Max Air da kuma UMZA Aviation Services Ltd.

Ya ƙara da cewa, kwamiti mai mutum 32 da aka kafa a ranar 26 ga Nuwamban bara ne suka zauna suka tantance kamfanonin, kafin suka amince da guda huɗun.

Sauran sun haɗa da mambobin hukumar NAHCON da ke wakiltar kowace shiyyar siyasar ƙasar nan, da shugabannin NAHCON na harkokin sufurin jiragen sama, da sayayya, da shari’a, da bincike na cikin gida, da ayyuka na musamman da kuma mamba mai wakiltar masana’antar sufurin jiragen sama.

Hakazalika, an zaɓo masu jigilar kaya guda uku don gudanar da ayyukan Hajjin bana. Su ne Aglow Aɓiation Support Serɓices Limited, Cargozeal Technology Limited da ƙualla Inɓestment Limited.

Shugaban ya taya kamfanonin da suka yi nasara murna tare da buƙace su da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda suka yi alƙawari a lokacin tantancewar.

A wani labarin kuma, Farfesa Abdullahi Sale Usman ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta aikin hajjin 2025 da ma’aikatar aikin Hajji da Umrah a madadin Nijeriya.

An gudanar da taron ne a ranar 12 ga watan Janairun 2025 a Jeddah Saudi Arabia domin gudanar da aikin Hajjin bana. A cikin tawagar shugaban NHCON akwai shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje, Sanata Abubakar Sani Bello; Shugaban kwamitin majalisar musulmi mai kula da aikin hajji Hon. Jafaru Muhammed Ali; Mai kula da harkokin Nijeriya a Riyadh, Dr Ibrahim Modibbo; Jakadan Nijeriya a Jeddah, Ambasada Mu’azzam I. J. Nayaya, da Ambasada Mahmud Lele daga harkokin ƙasashen waje.

Masarautar Saudiyya ta samu wakilcin mataimakin ministan Hajji da Umrah, Dr Abdulfatah Masahat a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar.