Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya musamman al’ummar Musulmi cewa babu wani mahajjaci da zai rasa tafiyarsa zuwa hajjin 2025 saboda ƙalubalen da ya shafi biza.
Ya kuma jaddada cewa, za a ɗauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba.
Ya umurci Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ta ɗauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba ga dukkan maniyyatan ƙasar nan.
Wannan dai shi ne sakamakon ganawar da mataimakin shugaban ƙasar ya yi da shugabannin hukumar a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Litinin.
Shettima ya kira taron ne biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa taƙaddamar kwangila da wani kamfanin Saudiyya Mashariƙ Al-Dhahabiah na iya haifar da hana alhazan Nijeriya biza.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, Shettima, ya fitar ta ce: “Ba za mu bari duk wani mahajjaci ɗan Nijeriya ya kasa zuwa aikin Hajjin 2025 ba. Aikin hajjin zai kasance babu ƙaƙƙautawa, kuma kowane ƙalubale za a magance shi cikin gaggawa”.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayar da kwakkwaran umarni ga shugabannin NAHCON, inda ya bukace su da su ɗauki dukkan matakan da suka dace don kare muradun alhazan Nijeriya, yana mai cewa “NAHCON dole ne ta yi duk abin da ya dace wajen tabbatar da halartar mahajjatan mu ba tare da wani shamaki ba.
Daga yanzu dole ne mu tsara matakan da suka dace, mu matsa kan hanyar da ta dace, mu yi aikin hajji ba tare da wata matsala ba.”
Da yake mayar da martani game da batun soke kwangilar da aka yi da kamfanin na Saudiyya, Shugaban NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa lamarin ba zai shafi aikin hajjin ba. “Babu wani dalili na fargaba. Ba za a bar wani mahajjaci daya mai rijista a baya ba,” inji Usman.