Hajjin bana: Ɗaurin watanni 6 da tarar Riyal 50,000 ga direban da ya yi jigilar alhazai ba tare da shaidar izini ba

Daga WAKILINMU

Sashen kula da sha’anin fasfo na Ƙasar Saudiyya ya yi gargaɗin cewa, duk wanda aka kama yana jigilar mahajjata ba tare da shaidar izini ba za a yi masa hukuncin ɗaurin wata shida a gidan kaso har da ƙarin tarar Riyal 50,000.

Baya ga wannan, sashen ya kuma ce za a bayyana sunayen masu laifin a kafafen yaɗa labarai na cikin gida tare da ƙwace abubuwan hawan da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.

Kazalika, hukumar ta ce duk wani mai aikin Hajjin da aka kama da laifin yin amfani da kan sarki (Stamp) na bogi wajen mallakar shaidar izinin Hajji, za a maida da shi ƙasara ba tare da ɓata lokaci ba, tare da haramta masa shiga Saudiyya na tsawon shekara goma.

Dokokin Ƙasar Saudiyya sun nuna duk wanda aka samu da aikata laifin da zai sa a hana shi shiga ƙasar, zai rasa damar sake shiga ƙasar na tsawon shekaru don wani aiki amma ban da Hajji da Umura.

Tun farko, sai da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ba da sanarwar za a ci tarar Riyal 10,000 ga duk alhajin da aka kama ya shiga Masallacin Ka’aba da Muzdalifa da Mina da dai sauran muhimman wurare, ba tare da shaidar izinin Hajji ba.

Ma’aikatar ta ce ɗaukar wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren da aka samar don yaƙi da yaɗuwar cutar korona a lokacin aikin Hajji.

Idan dai za a iya tunawa, ran 5 ga watan Yuli, hukumomin Saudiyya suka tabbatar da dokar hana shiga wurare masu muhimmanci ga waɗanda ba su da shaidar izinin Hajji.

Hukumar ta ce jami’an tsaro za su yi aikinsu a kan ɗaukacin hanyoyin birnin Makka da sauran wurare don gudanar da bincike da kuma hana take dokokin da aka shimfiɗa don Hajjin bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *