Hajjin Bana: Ɗaya daga cikin alhazan Nijeriya ya rasu a Makka

Rahotanni daga birnin Saudiyya sun ce, Allah Ya yi wa wani alhajin Najeriya, Alh. Muhammad Suleman rasuwa a Makka a ranar Lahadi.

Majiyarmu ta ce marigayin wanda dan asalin Jihar Kebbi ne daga yankin Karamar Hukumar  Argungu, ya rasu ne sakamakon fama da rashin lafiya.

Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Kebbi, Faruku Aliyu-Enabo, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema Larabai a Makka.

“Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da rashin lafiya, kuma an sallaci gawar a Masallacin Harami (Ka’aba), kana aka binne shi daidai da karantarwar Islama,” in ji Faruk.

Jami’in ya yi amfani da wannan dama wajen jajenta wa ‘yan’uwa da iyalan marigayin a madadin Gwanatin Jihar Kebbi.