Hajjin bana: Indonesiya za ta kammala yi wa maniyyatanta rigakafin korona a Mayu

Daga WAKILINMU

Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiyar Ƙasar Indonesiya, Oscar Primadi, ya ce gwamnati na sa ran kammala yi wa maniyyatan Hajjin bana allurar rigakafin cutar korona a watan Mayu mai zuwa.

Oscar ya faɗi haka ne yayin wani taron haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Harkokin Addini da Ma’aikatar Sufuri da kuma Majalisar Wakilai ta ƙasar, wanda ya gudana a ranar Litinin da ta gabata.

A cewarsa, “Duba da yanayin shirin bada allurar, muna da tabbacin da yardar Allah za mu kammala yi wa maniyyatan Indonesiya rikagafin ya zuwa Mayu.”

Ya ƙara da cewa, sai waɗanda suka kammala biyan kuɗin tafiya Hajjin bana kaɗai za a yi wa rigakafin.

Ya ce maniyyata dattawa 57,630 ne za a yi wa allurar a tsakanin Maris zuwa Afrilu, sannan sauran maniyyata 115,160 su samu tasu allurar tsakanin Afrilu zuwa Mayu.

Yana mai cewa, za a buƙaci maniyyata su gabatar da katin shaidarsu (ID card) da kuma shaidar da ke tabbatar da maniyyaci ya gama biyan kuɗin tafiya Hajji kafin a yi masa allurar.

A ƙarshe, Sakataren ya ce za a yi wa maniyyaci allurar ne a asibiti ko wata cibiyar kula da lafiya mafi kusa da shi.