Hajjin Bana: NAHCON da kamfanonin jirgin sama sun amince da ƙarin kuɗin Hajji $250

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Zikrullah Hassan, ya ce kamfanonin jirgin sama na cikin gida da aka amince su yi jigilar maniyyatan Hajjin bana, sun buƙaci a ƙara kuɗin Hajji da $250.

A cewarsa, kamfanonin da suka buƙaci ƙarin sun haɗa da Air Peace, Azman, Max Air da kuma Aero Contractors.

Ya ƙara da cewa, sun buƙaci hakan ne sakamakon rikicin da ke aukuwa a ƙasar Sudan, wanda hakan zai tilasta musu yin zagaye da tafiya mai nisan zango kafin isa Saudiyya a lokacin jigilar maniyyatan.

Wannan ne ma ya sa kamfanonin suka ƙi sanya hannu a yarjejeniyar aiki da NAHCON saboda ƙarin kasahe kuɗi da za su fuskanta saboda babu halin bi ta Sudan kamar yadda aka saba.

Da yake jawabi a wajen taron ƙara wa juna ilimi da aka shirya wa ma’aikatan NAHCON, hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kamfanonin jirgin sama a ranar Asabar a Abuja, Hassan ya bada tabbacin ba za a ɗora wa maniyyatan biyan cikon kuɗin ba.

“Bayan tattaunawa, kamfanonin jirgin samanmu sun amince da ƙarin $250 kan kuɗin jirgi don zuwa Hajjin bana.

“NAHCON, muna laluben dukkan hanyoyin da za su taimaka wajen warware wannan ƙari da aka samu,” in ji Hassan.

Haka nan, Hassan ya ce an ƙayyade ranar 25 ga Mayu a matsayin ranar da za a fara jigilar maniyyatan bana a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *