Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Al-Assad da iyalansa suna Birnin Moscow, kamar yadda hukumomin labarai a ƙasar Rasha suka bayyana, sa’o’i bayan ya tsere daga Siriya a lokacin da dakarun addinin Islama suka shiga Damascus.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Rashar, wadda ƙawa ce ga Al-Assad, ta kira taron gaggawa na majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) don samar da mafita bisa halin da ƙasar ta tsinci kanta aciki.
Tuni dai wani jami’an Gwamnatin Rasha ya tabbatar da cewa hamɓararren shugaban ƙasar da iyalansa sun samu mafaka a Moscow.
Rasha tare da takwararta ta Iran sune manyan masu goyon bayan Shugaba Assad.
Jami’an sojin Moscow sun taimaka wa jami’an Assad a shekarar 2015 a lokacin da aka yi yaƙi tsakanin su da ƴan adawa.
Haka kuma Rasha ta kasance a kodayaushe mai neman a samu mafita ta siyasa game da yaƙin Siriya inda su ke neman a shiga tattaunawa da MƊD.