Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sanata Rufa’i Sani Hanga ya bayyana cewa masu hamayya akan kujerarsa ta Sanatan Kano ta Tsakiya “in ba su yi hamayya ba, ba su yi halasci ba domin dama abinda ita siyasa ta gada kenan abinda rayuwa ta gada kenan.”
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a Kano, inda ya ce ba yadda za ka yi da ɗan hamayya mutum dole ko waye kai dole ka samu maƙiya da masoya, sai dai kullum fata shine masoya su fi maƙiya yawa.
Ya ce shi baya jin ciwon hamayya ko abinda ake faɗa duk abinda ake faɗa dama ƙa’ida ne a faɗa, suma in tasu ta kama suna faɗa, amma dai yanzu ana nan ana cin dudduniyarsa har murna ake in an je kotu ana cewa an karɓi kujera ana cewa har ma an karɓa an gama.
Ya ƙara da cewa shi tausayin masu faɗar wannna magana yake, saboda jahilci ne da rashin sani, domin wanda ya san yanda abin yake maganar za a karɓi kujerarsa ta Sanata ba ta taso ba.
Amma saboda ido ya rufe ya runtse ba sa ganin abubuwa yadda suke shi ya sa suke wannana, amma maganar karvar kujera ma ba a bi hanyar ta ba a cewarsa.
Ya ce saboda hujjoji da suka kawo bana hankali ba ne. Farko sun ce an yi maguɗi a zave a jihar Kano bayan a cikin kujerar majalisar tarayya 24 NNPP na da 18.
A sanatoci uku suna da guda biyu a ‘yan majalisar jiha guda 40 suna da 26 a ce kawai an ware shi a ce ya yi maguɗi.
Ya ce tazarar ƙuri’a da ya basu ta 288,000 ina za su kankare wannan a gwada cewa maguɗi ya yi wannan abu ne na vatan basira.
Sanata Hanga ya ƙara da cewa “‘Yan hamayya sun ma ce shi ba ɗan Jam’iyyar NNPP ba ne ya zo ya yi takara to in ma haka ne, ina ruwansu tunda su ba ‘yan jam’iyyar ba ne. Wannan in haka ne ɗan Jam’iyyar NNPP shi ya kamata ya kai qararsa.”
Ya ce ga shi ba ɗan jam’iyya ba ya zo zai takara, amma ina ruwansu ba suda wata harka da wannan, sun ɗauko takarda daga hukumar zaɓe wai ba sunansa.
Ya ce “Ni kuma na je na ɗauko musu littafi na ainihi daga mazaɓa da ƙa’idar doka abinda ta ce kowa ya je mazaɓarsa ya yi rijista na ɗauko littafin na kaiwa kotu na nuna mata nine na ashirin da wani abu a jerin sunayen, ba ni ne na ƙarshe ba, balle a ce yanzu aka je aka sani, sanan akwai sama da mutum 2000 a cikin rijistar nine na 23 ka ga duk wannan ɓatan basira ne da ɗimaucewa.”
Sanata Rufa’i Hanga ya ce ba abinda zai tayar masa da hankali tunda ya yi shari’a da su a kotun tarayya da ta ɗaukaka ƙara har zuwa kutun ƙarshe ta Allah ya isa akan wannan ya yi nasara, abinda ya yi nasara a kotun Allah ya isa kuma shine suka zo suka kai ƙara kuma.
Kotun ƙololuwa ta taɓa yin hukunci sannan wata ƙaramar kotu kuma ta zo ta juya shi? su suke ɓata lokacinsu shi ko a jikinsa.