Hana mata muƙaman gwamnati koma-baya ne ga siyasar Nijeriya – Ibrahim Haruna

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Wani matashin ɗan siyasa a jihar Gombe kuma mai kishin ganin an bai wa mata wannan kaso na 35 cikin ɗari da suke hanƙoron nema a muƙaman gwamnati daban-daban da na siyasa, Alhaji Ibrahim Haruna Tukulma, shugaban ƙungiyar nan da ba ta gwamnati ba ta Arewar mu duniyar mu, ya ce hana su matsayin zai mayar da siyasar Nijeriya baya.

Alhaji Ibrahim Haruna wanda har ila yau shi ne Sarkin Hausawan Tukulma, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a Gombe, inda ya ce mata ba ƙashin yasarwa ba ne a siyasar Nijeriya, don haka a ba su wannan kaso da suke nema don a ci gaba da damawa da su a siyasance ganin cewa suna da rawar takawa.

Tukulma, ya kuma ce a sanin sa ƙasashen duniya da dama da suka ci gaba waɗanda su suka kawo wannan mulki na siyasa suna yi da mata to me ya sa mu a Nijeriya ake ƙoƙarin ganin an yasar da su bayan kuma su ne ƙashin bayan ci gaban al’umma da ma siyasar.

A cewar sa ya lura ya ga ko muƙamai na takara a siyasa ba a so a bai wa mace saboda amfani da ake yi da addini amma kamar yadda ya ce hakan ai ba kamata ba domin duk da cewa ƙasar akwai addinai daban-daban kuma ana ganin Musulunci ne ke da rinjaye ya sa ake ganin bai kamata a cewa mace ta yi shugabanci ba ba dai dai bane tunda da tsarin kundin mulki ake aiki ba Alƙur’ani ba.

Ya ƙara da cewa yanzu idan ba a ja matan a jiki sun fito sun shiga siyasa ba, kuma suna samun muƙamai ta yaya za a yi a ja hankalin su su gane suna da muhimmanci da rawar takawa a tsakanin al’umma.

Sarkin Hausawan Tukulma, ya ƙara da cewa ko a ƙasashe irin su Ingila da Amurka da Jamus da ake koyi da su a siyasa har shugabanin ƙasa mata sun yi kuma sun taka rawar gani sosai fiye da wasu mazan, irin su Margret Tacha da Angela Markel da sauran su.

Daga nan sai ya yi kira ga mahukuntan ƙasar nan da cewa su duba su gani hana matan wannan dama zai haifar da matsala domin hakan zai sa su ji ba su da amfani fitowar su ma bai kamata ba sai ka ga hannun agogo ya koma baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *