Hana sana’ar acaɓa a Nijeriya: Gwamnati za ta rasa kuɗin shiga mai yawa

  • Yayin da ta’addanci zai ƙaru, cewar Hajiya Hauwa Inuwa

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Hajiya Hauwa Muhammad Inuwa, tsohuwar ‘yar takarar kujerar Sanatan Gombe ta Arewa a Jam’iyyar Accord ta ce tana mai kira ga gwamnati da ta janye ƙudurinta na hana sana’ar Acaɓa a Nijeriya domin kar a jefa mutane cikin ƙuncin rayuwa.

Hajiya Hauwa Inuwa, ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a Gombe, inda ta ce masu sana’o’i daban-daban guda 7 ne suke cin abinci a dalilin babura: Akwai masu faci, masu sayar da baƙin mai da makanikai da masu wanki da sauran idan aka hana ya za a yi da su.

Ta ce idan gudun ta’addanci ne an san inda ‘yan ta’addan suke a daji an kuma san yadda za a yi a kama su; ba a neme su an kama su ba sai masu neman halak ake ƙoƙarin hanawa mene ne ranar yin hakan so ake a taru a koma ‘yan ta’adda baki ɗaya.

Hauwa, ta kuma ce gwamnati ta janye wannan aniya nata sannan kuma ta inganta wutar lantarki don a gina masana’antu da kamfanoni da zai ƙara rage zaman banza.

A cewarta idan aka ci gaba da ƙure talaka har ya kai bango hakan ne ke sa ya shiga ayyukan ta’addanci don nemawa kan sa mafita, wanda a cewarta da haka ne masu garkuwa da mutane ‘yan fashin daji suka samu sana’a har suka yi ƙarfi.

A ɓangare ɗaya ta yi kira da su matasan da cewa suma kar su dogara a sana’a ɗaya a raba hannu a samu wata sana’a a haɗa don a rufawa juna asiri, saboda a cewarta koda an hana acaɓa mutum ba zai shiga wani hali ba.

Daga nan ta ce hatta ita gwamnati kan ta za ta yi asara domin masu sana’ar suna biyan ta haraji na kuɗi mai yawa wanda hana su ɗin zai rage mata hanyar shigar kuɗi.