Hana wani, hana kai: Kanawa me yake damun ƙwaƙwalenmu ne?

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI

Hassada! ƙyashi! Mugun baki! Sun jawo abinda ya samu ‘yar uwarmu Maryam Shetty na alheri sai da aka yi mata sanadin da ta rasa, mu ma kuma muka rasa.

Wasu za su ce ita ce dai ta rasa amma mu bamu rasa ba! To Wallahi mu ma mun rasa!.

Maryam Shetty Matashiyar ce kamar yadda muke ta ƙarya da Ihun cewar; mun gaji da Mulkin Tsoffin nan da suke gana mana azaba. Yanzu muna son matasa su ma su fito a dama da su. Maryam Shetty ta samu damar da za a dama da ita a matsayinta na matashiya kuma ‘yaruwarmu musulma. Amma abin mamaki muka dinga aibata wannan alherin.

Ya nuna a zahiri kenan cewar ƙarya muke ba canjin muke so ba. Kawai canjin da muke faxa a baki ne. mun fi son tsofaffin da suka saba yin sukuwar hawan Sallah a kanmu su cigaba da yin sukuwar a kanmu har zuwa lokacin da Mahdi zai bayyyana.

Wani abu da ba ku sani ba da kuka dinga jifan Maryam Shetty da cewar; yarinya ce kuma ‘yar Soshiyal Midiya ce. To shi ne me? Ai yarinyar za ku fi amfana da muƙamin da ta samu domin za a samu sabon tunani ba kamar na tsoffin ba. Sannan idan Maryam Shetty ce ta samu, ‘Yan Soshiyal Midiya ɗin su ma za su samu ta ɓangaren ta ko ba ta ba ka ba, in ta ba wa wani ka ga ai an samu cigaba, duk da na ga yanzu siyasar tamu ta koma ta Allah ya sa wanda na sani ya samu ba wai mai nagarta ya samu ba.

To Yanzu dai ga dattijuwa nan kun samu Shugaban Jam’iyyar APC na rikon ƙwarya ya yi maƙarƙashiya an cire sunan Maryam Shetty ya saka tasu. Kun ga ai surutanku a Soshiyal Midiya na cewar; Maryam Shetty ba ta dace da muƙamin Minista ba ya jawo muku. Yanzu duk wasu kuɗaɗen da za a ba wa Jihar Kano ta hanyar Minista za su fara zuwa hannun Uwargidan Shugaban Jam’iyyar ne sannan su zurare cikin aljihun babbar riga wadda ba ta qoshi da tara Dala. Kun ga ai kun yi wa kanku da kanku mugunta. wanda ake cewa: “Hana wani, hana kai!

Sauran Jihohi an ba wa Matasa mata waɗanda ba su kai Maryam Shetty ba. Amma babu wanda ya soke su a kan rashin dacewa. Ko a Katsina Cibiyar Hausa an ba wa Hannatu Musawa ba ta da aure kuma babu wanda ya ce ba ta cancanta ba. A baya an yi Hajiya Sadiya daga Jihar Bauchi Ministan Buhari ba ta da aure, babu wanda a Bauchi ya ce ba ta dace ba. A Kaduna ma an yi.

A wannan zubin na Alhaji Bola Ahmad Tinubu an yi a Jihar Edo, inda aka ba wa Dakta Betta Edu. ‘yar Soshiyal Midiya ce ita ma babu wanda ya ce ba ta cancanta ba. Sai mu Kanawa?!

Don Allah idan wani abu na alheri ya samu ɗan’uwanmu mu daina hassada da ƙyashi da nukura!.

Abdullahi Jibril Larabi (UNCLE LARABI), mai sharhi ne a kan al’amuran siyasa na yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.
Lambar waya: 08065418892