Hankalin ‘yan siyasa ya raja’a ga zaɓen gobe na Anambra

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zuwa yanzu dai hankalin kowane ɗan siyasa da masu fashin baƙi akan al’amuranta ya koma kan zaɓen gwamnan Jihar Anambra, tun bayan da jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taron ta a Asabar da Lahadin makon jiya a Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda mutane da dama, ciki har da jam’iyya mai mulki ke musu shaguɓe da habaicin taron ba zai yiwu ba, saboda rikice-rikicen da ke cikin gidan jam’iyyar.

Me ya yi saura yanzu? Sai zaɓen jihar Anambra, wanda shi ne madubi a wajen ‘yan siyasa a cikin satin nan, wanda kuma ma tun lokacin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar da sanarwar irin kimtsawar da ta yi da kuma irin matakan da ta ɗauka na gudanar zaɓen, sai kuma Ƙungiyar IPOB masu rajin kafa ƙasar Biyafara suka fara tada jijiyar wuya da yamutsa hazo na cewa zaɓen bai yiwu ba, inda suka ayyana cewa babu mahalukin da ya isa ya gudanar da zaɓe a jihar matuƙar ba a sako musu jagoransu Nnamdi Kanu ba, wanda ke fuskantar shari’ar cin amanar ƙasa da haddasa tashin hankali.

A gefe guda kuma, INEC ta mayar musu da martani cikin karsashi da nuna musu cewa ita fa ba ta kansu ma take ba, domin ta shirya wa zaɓen babu gudu ba ja da baya, babu kuma wani ko wata ƙungiya da za ta hana gudanar da zaɓen na gobe Asabar. 

Kazalika hukumar ta INEC tun kwana biyu kafin zaɓen ta fito fili ta bayyana wa jama’a irin salon da ta ɗauka da kuma kayayyakin da za ta yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen tare da tsaurara tsaron kare kayan aikinta masu hatsari waɗanda za ta yi amfani da su a zaɓen don gano kayan jabu.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da ya yi da masu ruwa da tsaki a zaɓen a Awka, babban birnin jihar.

Yakubu ya yi gargaɗin cewa hukumar za ta ɗauki matakin shari’a a kan duk wanda ya aikata laifin maguɗi a zaɓen, ciki har da duk wani ma’aikacin zaɓe da aka kama da hannu a ciki.

Ya ce, “Ina so in tabbatar wa da dukkan masu zaɓe a Anambra cewa a wajen tsara kayan zaɓen masu hatsari, hukumar ta saka ƙarin wasu alamomin tsaro waɗanda ba a gani da ido, ciki har da kalolin sirri mabambanta.

“Haka kuma an tsara kayan aikin ne bisa kowace ƙaramar hukuma da rumfar zaɓe.

“Saboda haka bari in gargaɗi duk wani wanda zai yi ƙoƙarin yi wa tsarin zagon ƙasa cewa mun tanadi isassun matakan rigakafi don gano kayan bogi. “Za in wanda zai zama sabon gwamnan Anambra ya na hannun masu zaɓe kuma tilas ne zaɓin su ya yi galaba.”

Shugaban ya kuma tunatar da jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya bayan su cewa har yanzu sayen ƙuri’a laifi ne a dokar ƙasar nan.”
Ya nanata cewa har yanzu dokar hana amfani da wayar hannu ko wata na’urar ɗaukar hoto a rumfar zaɓe ta na aiki.

Ya ce, “Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, waɗanda membobin Kwamitin Tuntuɓar Hukumomi kan Tsaro a Zaɓe ne, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’, za su tura ma’aikatan su domin kama masu karya doka tare da gurfanar da su a kotu.”

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su da su roƙi magoya bayan su da su kauce wa furta munanan kalaman ko yin wani abu da zai kawo tsaiko kafin zaɓen da lokacin da ake yin sa da kuma bayan sa.

Ya ce, “A yayin da mu ke aiki tare da hukumomin tsaro, mun kuma yi abubuwa masu daman haske don tabbatar da an yi zaɓen nan cikin nasara.

“Don Allah ta hanyar kalaman mu da ayyakan mu mu mara wa shirin wannan zaɓe cikin lumana da inganci goyon baya.”

Yakubu ya yi la’akari da cewa an rarraba kayan zaɓe marasa hatsari a dukkan yankunan ƙananan hukumoni 21 na jihar.

Ya ce, “Za a kai waɗannan kaya zuwa yankunan rajista ko unguwanni a ranar Juma’a don a samu bu e rumfunan zaɓe da ƙarfe 8.30 na safe a ranar zaɓe, wato Asabar.”

Yakubu ya ce Anambra za ta kafa tarihi a matsayin jihar farko a Nijeriya da aka yi zaɓen gwamna inda hukumar ta yi amfani da tsarin tantance mai zaɓe ta hanyar komfuta, wato ‘Biometric Voter Accreditation System’ (BVAS).

Ya ce, “Ina farin cikin shaida maku cewa dukkan na’urorin BVAS da ake buƙata don yin zaɓen a ranar Asabar an tsara su an kawo su Anambra.

“Ma’aikatan zaɓe kuma an horas da su kan yadda ake amfani da na’urar, sannan mu na da isassun ma’aikatan kula da na’urori da za su gyara duk wata mishkila da ka taso.”

Yakubu ya yi kira ga sababbin masu zave waɗanda aka yi wa rajista ko waɗanda su ka buƙaci a ba su katittikan zaɓe na dindindin, wato ‘Permanent Voter Cards’, kuma waɗanda ba su karɓa ba da su hanzarta su karɓa.

Ya ce, “Ina farin cikin sanar da ku cewa an buga katittikan zaɓen kuma an kai su kowace ƙaramar hukuma don masu zaɓe su karɓa.

“Haka kuma mun tuntuɓi masu zaɓen ta hanyar tes da imel, mun sanar da su ainihin inda za su karɓi katittikan su.”
Yakubu ya tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki cewa hukumar sa ta shigo da na’urorin musamman da za su taimaka wajen agaza wa naƙasassu a wajen zaɓen.

Jiya Alhamis ne dai dukkanin ‘yan takarar da ke neman kujerar gwamna a Jihar Anambrar suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Awka, babban birnin jihar, inda kuma suka sanya hannun kan idon Shugaban Hukumar Zaɓe ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.

Kwamatin gina zaman lafiya na National Peace Committee ne ya shirya taron, ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa Abdulsalami Abubakar.

Daga cikin ‘yan takarar akwai Ifeanyi Uba na jam’iyyar YPP, Andy Uba na APC, Chukwuma Soludo na APGA, Valentine Ozigbo na PDP, Godwin Maduka na Accord Party (AP), sai kuma Etiaba Chukwuogo na Action Alliance (AA).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *