Hanyar da ASUU za ta gamsar da ɗalibai

A duk lokacin da ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki takan yi iƙirari ne da yanayin jami’o’i da kuma ɗaliban cikinsu.

Haƙiƙa da yawa daga cikin ɗalibai sun rasa irin wannan kishi da ƙungiyar ASUU take yi musu. Sau da yawa wasu ɗalibai masu gajeren zangon tunani iri na, na kallon rigimar ASUU da gwamnati a matsayin rigima ce kawai irin ta ‘ya’yan turaka, domin duk daga kwasfo ɗaya suka fito, rigima ce tsakanin masu wukar yanka da masu aska kawai.

Sanin kowa ne a wannan ƙasa, farfesoshi ne ke yin aikin ‘returning officers’ na kafa irin waɗannan shugabannin da ba su san darajar ilimi ba. Idan ƙungiyar ASUU tana son ta tabbatar wa ɗalibai cewa don su take yi, to ta hana duk ‘ya’yan ƙungiyarta shiga don taimakawa zaɓe mai zuwa, su hana kowane farfesa yin aikin ‘returning officer’ ko da kuwa an cimma matsaya tsakaninsu da gwamnati, wannnan ya zama matakin horo ga gwamnati.

Daga lokacin ne gwamnati za ta girmama matsayinsu, kuma ɗalibai su yarda da cewa don su suke yi.

Matuqar ƙungiyar ta ƙasa yin haka, kila saboda kwaɗayin dan na goro da suke samu a lokutan zaɓe, to kuwa za a cigaba da kallonsu a matsayin gurɓatattun da kan samar da gurɓatattun shugabannin da kan haifar da gurɓacewar ilimi.

Daga SANI SHEHU LERE, 08062798146.