Hanyoyi biyar da za ki iya sa idonki haske cikin sauƙi (1)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja, fatan kuna samun biyan buƙata daga ababen da muke kawo ma ku a kowanne sati. Mun gode da irin ƙwarin gwiwa da kuke ba mu.

A yau shafin kwalliya zai taɓo ɗaya daga cikin muhimman ababen da ke ƙawata kwalliya kuma yake sanyata fita sosai ko da kuwa ba a tsananta a cikinta ba, wato hasken ido wanda masu iya magana suka ce, ya fi hasken zinariya.

Sananen abu ne, hasken ido na da matuƙar muhimmanci a kwalliya musamman ma ta fuskar mata, domin sukan haskaka fuska, su sanya ma’abuci kallon su a nishaɗi.

Duk da cewa, idanuwanmu na canzawa a lokacin da yanayin jikinmu ya fara canzawa ta sanadiyyar shekaru. Ba kuma kawai a iya ƙarfin aikinsu wannan canji ke tsawa ba, ya kan shafi har yanayin hasken da suke da shi. Wani lokacin sukan yi duhu ko dimuwa da sauransu.

Kafin komai, yana da matuƙar muhimmanci sanin matsalar disashewar hasken ido ba ta buƙatar barin cin wasu ababe ko yawan atisaye don magance ta, sai dai amfani da wasu hanyoyi da za su iya sa idon haske ko su kawar da duhun da suka fara yi ta sanadiyyar shekaru.

Wani abin farin ciki kuwa, idanuwa ba sa cikin ɓangarorin jiki da kwalliyarsu ke cin kuɗi da yawa, domin ababen gyara ko haskaka ido masu sauƙi ne da ba a shan wahala yayin aiwatar da su. Kuma bibiyar su zai taimaki ido na tsayin shekaru ko da kuwa a zamanin manyantaka.

Ga wasu daga cikin hanyoyin haskaka ido.

  • Gurji (cucumber):

Kasancewar kokwamba na ɗauke da ruwa masu yawa ne ya sanya ta shiga cikin jerin ababen da amfani da su yake wanke ido, ya hana duk wani dalili da zai iya disashe su. Kuma tana ɗauke da sinadarin da ke murƙushe duhun zagayen ido, wanda ke samuwa dalilin rashin barci, gajiya da kuma shekaru. Yawan cin kokwamba safe da dare, yana taimako sosai wurin haskaka ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *