Hanyoyi biyar da za ki iya sa idonki haske cikin sauƙi (2)

Daga AISHA ASAS

  1. Gashin ruwan sanyi:

Sanya abu mai sanyi-sanyi a ido na taimakawa ido musamman ga waɗanda wani yanayi ya sanya idonsu yin ja, kamar ciwon ido, bigewa da sauransu. Akan yi hakan ne da tsaftatacen ƙyale, a dinga sanya shi a ruwan sanyi ana matsewa, kafin a ɗora shi a ido.

Amma ba a buƙatar matsa idon kamar yadda ake yi wa gashin jiki na ruwan zafi. Idan ka kwantar da kanka a kujera ko hilo, sai a ɗora ƙyallen mai sanyi a saman idanuwan, a bar shi har ɗan sanyin ya ratsa idon, sannan a sake maimaita wa.

Abin lura, yana da kyau a kula da yanayin da ake ciki na zafi ko sanyi wurin irin ruwan da za a amfani da su don gujewa haifar wata cuta. Yin hakan ga ido lokaci-lokaci zai haskaka ido tare da kawar da duhun da ya yi.

  1. Barci mai yawa:

Shin kuna da masaniyar ƙarancin barci na ɗaya daga cikin ababen da ke haifar da duhun ido. Kuma yana hana duk wani yunƙuri na ganin an haskaka su tasiri. Idan ana samun barci mai yawa kamar awa bakwai zuwa sama shi kansa wani hanya ne na sama wa ido haske. Rufe idon yayin barcin na ba wa idon damar tsarkake kansa tare da ƙoƙarin mayar wa idon sahihin haskenshi.

Ga waɗanda ke da matsalar rashin barci, zan ba su shawarar amfani da hanyoyi don ganin sun dinga yin barcin yadda ya kamata, kamar yin wanka duk lokacin barci, ko yin atisayen dare don jiki ya yi saurin buƙatar barcin da sauransu.

Kada a yi amfani da magunguna don magance wannan matsala, domin za su iya kawo matsala ga jiki da ma ƙwaƙwalwa, wanda zai iya kai ga barcin ya dogara kawai kan maganin, ma’ana ba ya zuwa har sai an sha. Hakan na nufin ba ka nema wa kanka magani ba, an samar wa matsalar takwara ce.

4.Shan ganyen shayi:

Ganyen na’ana’a ko nau’ukan baƙin ganye (Black tea) na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke kawo hutu ga jiki, wanda ga wasu ya zama ɗabi’a shan su kafin yin barci, don samun natsuwar jiki.

Sai dai shan shayi daga waɗannan na daga cikin hanyoyin haskaka ido, domin yadda yake ba wa gangar jiki hutu, haka yake ba wa ido, wanda ke taimakawa ƙwayoyin hallitun da ke kula da idon wurin dawo da hasken idon zuwa lokacinsa mafi kyau.

Kazalika, wannan hanya ce ta inganta lafiyar idon, domin yana hana yawaitar ƙwayoyin cuta da ke sanya ƙaiƙayin ido, wanda zai haifar da jan ido ta sanadiyyar sosawa.

  1. Yawan cin ganye da ‘ya’yan itace:

Bincike ya tabbatar koren ganye na ɗaya daga cikin manya-manyan hanyoyin wanke ƙwayar ido, domin yana ɗauke da sinadaran da ke wanke ido, ba ma kamar waɗanda aka sasauta yayin dafa su, ko ake cin su a yanda suke, kamar latas, kabeji da sauransu.

Kasancewar ganye da kayan itace manyan jarumai da ke ɗawainiya da ɓangarori da yawa na jiki, ba zai zama abin mamaki ba idan an ce a irin tallafin da suke ba wa jiki har da ido wurin haskaka su tare da kawar masu da ƙwayoyin cutar da ke hana su sakewa. Kazalika, waɗannan ababe guda biyu na wanke ƙoda sosai.

Lafiyar ƙoda kuwa wata hanya ce ta sama wa ido haske, domin zaman ƙoda a matsala kawai na iya haifar da disashewar ido. Kuma ta sanadiyyar raunin aikin ƙoda ne ke sa ido ya rasa isasshen sinadaran da yake buƙata waɗanda ke fitowa daga abincin da muke ci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *