Harƙallar nukiliya: Iran ta ƙi amincewa ta tattauna da Amurka da Turai

Daga AISHA ASAS

Ƙasar Iran ta ce ba yanzu ne lokacin da ya dace a yi magana kan batun makaman nukiliya ba duba da halin da ƙasashen Amurka da Turai suka nuna.

Iran ta ƙi amincewa da ta yi zaman tattaunawa da ƙashashen Amurka da Turai domin tattauna yadda za a farfaɗo da yarjejeniyar nukilya ta 2015, tana mai cewa dole sai Amurka ta ɗage duka takunkuman da ta ƙaƙaba mata kafin ta amince.

A cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, la’akari da halin da Amurka da wasu ƙasashen Turai suka nuna, ya sa Iran ba ta ga dacewar tattauna da ƙasashen ba kamar yadda Tarayyar Turai ta buƙaci a yi.

Amurka ta ce wannan abin ɓacin rai ne amma a shirye take ta sake shiga tattaunawar diflomasiyya domin cim ma fahimtar juna wajen farfaɗo da harƙallar makaman nukiliya ta JCPOA.

Jami’an Iran sun ce ƙasar Tehran na nazarin tayin da babban jami’i na Tafayyar Turai, Josep Borrel ya aike da shi na neman a yi wani zaman tattaunawa ba a hukumance ba tare da sauran ɓangarorin da lamarin ya shafa ciki har da Amurka wadda ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumi bayan shugabanta na wancan lokaci, Donal Trum ya yi fatali da batun nukiliyar a 2018.

Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a 2015, Iran ta juya wa lamarin baya tare da neman a ɗage mata takunkuman da aka kafa mata kafin ta amince ta bada haɗin kai. Amma tun bayan da Amurka ta janye jikinta daga yarjejeniyar kana ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai sakamakon matsin lambar da ta sha game da yaƙi da ƙasar Tehran, daga bisani Iran ta koma ta ci gaba da harkar nukiliyarta wanda hakan ya saɓa wa JCPOA.

Iran da sabuwar gwamnatin Amurka ƙarkashin Joe Biden, sun yi ta samun saɓani kan wanda ya dace ya shige gaba wajen farfaɗo da yarjejeniyar. Amma Iran ta ce atabau sai Amurka ta janye duka takunkuman da ta kafa mata, yayin da ita Amurka ke ra’ayin cewa sai Tehran ta dawo ta bada haɗin kai tukuna.