Har mai sayayya a yanar gizo na da damar kai ƙorafi hukumar kula da haƙƙin kwastoma a Kano – Hon. Nasiru Na’ibawa

Hon. Nasiru Usman Na’ibawa shi ne Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kano na Musamman kan yadda hukumar Karota da Kwanzuma ke ciki a fagen yin ceto rayuwar al’umma daga halaka tun daga abin da za su ci ko su yi mu’amala zuwa titinan da suke zirga-zirgar yau da kullum. Ga yadda tattaunawarsa da Wakiliyar Manhaja, Bilkisu Yusuf Ali, ta kasance:

Me za ka fara da shi game da Hukumar Karota ta Jihar Kano?
Ita wannan hukumar ta Karota hukuma ce da aka kafa ta bisa doka tun a tsohuwar gwamnatin Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso wadda aka kafa ta kan raguwar cunkoso da samar da doka da oda akan hanyoyinmu don magance haɗura akan hanyoyinmu sannan da samar da ayyukan yi ga matasa da tabbatar da ana bin ƙa’idojin tuƙi a wannan jiha tamu. Ita wannan hukuma tana da shugaba wato MD da sauran ma’aikata na sashi–sashi wanda tsohon zaɓaɓɓen ɗan majalisar jiha kuma tsohon majority leader Baffa Babba Ɗan’agundi kuma tana da ma’aikata tun daga kan DAGS akwai DG akwai kotu da ke ladaftar da masu laifi. Tunda mai girma gwamna ya na]a wannan shugabanci na Honourable Baffa Babba ake durfafi aiki babu dare babu rana mutane kuma sun zama shaida kan hakan na abubuwan alheri da wanna hukuma ta samar. A tashin farko mun tarar da motoci guda biyu ne suke aiki yawancinsu sun lalace, amma tsayiwar daka na shugaban hukumar aka gyara wasu aka samar da wasu ina tabbatar miki wannan hukuma tana da motoci tun daga hilos da manyan motoci mac waɗanda suke ɗaukar motoci da sauransu. Aƙalla a yanzu muna da motoci sun kai guda hamsin, an gyara wasu an sayi wasu. waɗanda suke fita aiki ba dare ba rana. An gyara ofishin wannan hukumar an inganta ma’aikatanta an samar musu da sababbin unifom da takalma da kayan sanyi da rigar ruwa don dai tabbatar a kowanne irin yanayi ma’aikatanmu suna aiki cikin nutsuwa da tsafta. An rage yadda ake karɓar cin hanci da rashawa da makamancin irin wannan.


Sannan a matsalar cinkoson tasha, misali tashar gadar lado an san yadda ake yin awa biyu har fiye a gosilo amma wannan hukumar ƙarƙashin jagorancin MD ɗinta Hon Baffa Babba Ɗan’agundi sai da aka tabbatar sun tashi a wurin sun koma tashar Na’ibawa wanda yanzu ya zama tarihi. Idan aka je Mega Hotoro round about wadda ake lodi ita ma kuma tana haɗa goslow amma yanzu sun tashi sun koma ainihin tashar da ta ke a Mariri. Sannan Haɗeja road waɗanda suke lodi a shatale-tale suma an tashe su sun koma tashar ‘Yankaba. Haka BUK Kabuga suma tashar nan da ke kashe hanya suma sun koma tashar Rijiyar Zaki. Abubuwa da yawa an yi su don tabbatar da ingancin tsaro a jiharmu. Haka ko’ina za a ga ma’aikatan wannan hukuma suna aiki don rage cunkoso. Suna sauyi /shipting kala uku wasu da safe wasu da rana wasu da daddare. Matuƙa adaidaita sahu an samar musu na’ura da ake kira Tiraka wanda amfaninta yana da yawa daga ciki an ƙaranta yawan sace-sace da ayyukan ta’addanci da ɓatan kaya da sauransu. Duk wannan ci gaba ya samu ne ƙarƙashin shugabancin MD Hon Baffa Babba Ɗan’agundi. Da wasu da yawan gaske , gaskiya ci gaban ba zai lissafu ba a ƙanƙanen lokaci.

Ayyukan Karota da ma ya taƙaita ne kawai a kan tituna?
Eh shi ne dai babban aikinsu sai dai a yanzu mai girma gwamna ya sa su a cikin kwamitin tsaro na jiha wanda duk mitin da ake yi shi shugaban wannan hukuma yana ciki. Don haka duk wani abu da ya tashi wanda za a bayar da gudummawar tsaro za a ga wannan hukuma ta Karota a ciki. Haka akwai abubuwan Tax force nan ma kina iya ganin ma’aikatan Karota kamar karɓar haraji da sauransu don board of internal revenue suna iya neman kariya kuma maigirma gwamna ya sa shugaban karota a hukumar.

Daga kafa Karota zuwa yau kana ganin an yi nasara a abin da aka ɗauke su don shi?
ƙwarai kuwa, kwalliya ta biya kuɗin sabulu don ko ke aka tambaya daga gidanki zuwa nan ofishina a baya sai ki yi awanni ba ki ƙaraso ba amma a yanzu ko minti sha biyar ba ki yi ba daga fitowarki zuwa nan kin ga kuwa ke ma shaida ce. In ki ka je Bata ko Kasuwar rimi ko kasuwar Tarauni ko gadar Lado da sauran wurare da a baya da mai tafiya a ƙafa da mai tafiya a mota ko keke ko babur ke tsoro da fargabar bi yanzu a guje zai zo ya wuce komai ya daidaita. Sannan samarwa matasa abin yi shi ma ba ƙaramin ci gaba ba ne. Ma’aikatan karota kusan dukkaninsu matasa ne.

Duk abin da aka ce matasa ne ziryan za a samu rawar kai da abubuwa na rashin nutsuwa ko tarbiyya ya ake a Karota?
Da yake tsarin da ake bi ana iya kiransa da Para military wanda tana bin tsari na ladaftarwa akwai oc da sauran muƙamai akwai masu igiya da marassa igiya da masu star ɗaya da biyu ya danganta da dai yadda ka shigo aikin tunda wani an ɗauke shi da sakandire wani da diplpma wani NCE wani digiri ya dai danganta da yadda ka shigo kuma akwai shugabanci a kowanne unit shi yasa ake zaune lafiya.

Hotunan da ke yawo a kafar sadarwa na kama kayan masarufi da al’amuran yau da kullum kamar magani shi ma aikin Karota ne?
Tun farko hukumar Karota memba ce a cikin task force na tabbatar da cewa ba a sayar da gurɓatattun magunguna a wannan jihar ba, ana nan kuma sai Allah kuma cikin hukuncinsa mai girma gwamnan Kano ya ba wa Honourable Baffa Babba Ɗan’agundi ya riƙe wata hukuma mai suna Kano State Consumer protection council wato hukuma mai kare haƙƙin mai saye da me sayarwa inda ni Hon Nasiru muke aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayina na SSA na hukumar karota kuma ita ma hukuma ce mai zaman kanta da aka ba shi tare da bijiro da ayyuka tunda ma’aikata ce da ke da tsarinta na musammam da ma’aikatanta ita ma kuma tunda Karota tana daga cikin wannan task force kuma ita hukumar an ce shi Hon Baffa ya riƙe shi ya sa za ki ga muna aiki kafaɗa da kafaɗa tare da su don tabbatar da cewa an samu nasarar daƙile gurɓatattun abubuwa misali in ki ka duba watanni uku da suka wuce an yi wata annoba ta ko ibtila’i na ɗan tsami ita wannan hukumar ita ta yi ta bibiya tare da kakkama kayayyakin da ba su da inganci a wannan jihar tamu ta Kano musamman waɗanda wa’adinsu ya ƙare (expire) wanda a watannin nan uku mun kama kaya sun fi katan dubu talatin marassa inganci.

To a shagunansu suke ƙarewa saboda rashin saye da ba a yi ba?
Wasu ai a haka suke sayo wa sun san ya ƙare ]in. Wasu kuma sai a gaɓar yana ƙarewa suke saya wasu kuma a hannunsu ya ƙare ɗin amma ba su fitar da shi ba. Mun sami ha]in kai kwarai daga shugabannin kasuwannin jihar Kano sannan jama’ar jihar Kano suna ba mu kyakkyawar kulawa da goyon baya da haɗin kai sannan akwai masu kawo mana labari wato informers kuma mu a ɓangarenmu duk wanda ya kawo mana labari muna bas hi na goro.

Idan kuma to mutum sai bayan ya sayi kaya ya biya ya tafi sannan ya lura wa’adinsu ya ƙare ya zai yi?
Ai ƙofar wannan hukuma a buɗe take ya kawo ƙorafinsa a bi masa , ai da ma sunan hukumar kare haƙƙin mai saye da sayarwa kuma ba iya kayan da suka yi expire ba ne ko kayan dab a su da inganci ba ne hatta riga ko atamfa ko shadda in ka saya a matsayin cikkakken cotton sai a ka ba ka leda ko lanon ko aka ba ka wadda darajarta ba ta kai wadda ka saya ba in dai ka koma a biya ka ba su biya ba to kana da haƙƙi da dama ka kawo su wannan hukuma don aikin hukumar ne kwato haƙkin mai saye da sayarwa kuma za a bi haƙƙi.

Hukumar na da kotu ne?
Ai doka ce ta ba wa hukumar dama da iko na ta daidaita tsakanin mai saya da sayarwa.

Akwai kasuwanci na yanar gizo-gizo da ake yi ka sayi abu idan an tashi kawo ma sai ka ga ba shi ba ne ana iya kawo wa wannan hukumar ƙorafin?
In dai akan ƙa’ida aka yi kuma kamfani ne rayayye akwai shi kuma ka saya ka biya kana da shaidar rasitin kamfanin kuma aka kawo maka baa bin da ka siya ba za ka iya kawo kokenka wannan hukuma a bi ma haƙƙinka.Kai hatta warranty da ake bayar wa in ka sayi firji ko waya na shekara guda in har ka tabbatar kai ba kai ka lalata ba kana da iko in ka je ba su sauya maka ba kana da iko ka kawo ƙorafinka a bi ma haƙƙinka. Misali ko a kwanann nan mun kakkama baƙin mai wanda ake yin algus kuma mun ɗau mataki.

Me ya janyo wannan nasarar da ku ke samu ?
Matakin nasararmu shi ne goyon bayan gwamna. Mai girma gwamnan jihar Kano yana matuƙar alfahari da wannan hukuma shi yasa a kowanne lokaci yake ba ta goyon baya na duk abubuwan da ya kamata na wannan hukuma na ta motsa da wanda aka nema da ma wanda ba mu nema ba wannan hukuma ana samunsa. Sannan shugabanta Hon Baffa Babba shi ma mutum ne jajirtacce kuma tsayayye yana bibiyar duk abin da ake yi.

Wanne abu ne ya taɓa ba ka mamaki a irin wannan kamen da ku ke yi?
Ni abin da ya fi ba ni mamaki shi ne a ce mutum da yake da iyali da ‘yan’uwa amma a ce ya sayar da abubuwa marassa kyau wanda zai iya shafar lafiyar al’umma har ma ta kai su ga halaka. Misali akwai lokacin da tashi guda muka ɗauki katan dubu ɗaya ɗari tara da casa’in da huɗu a wuri ɗaya na wa’adin omo da ya ƙare akwai inda muka je muka ɗauki power oil na man gya]a katon wajen ɗari biyu day a lalace ya yi expire mun kama sigari da ake sha wadda katan dubu tara wadda wa’adinta ya ƙare wadda shan ta ma da kyanta yaya aka ƙare bare wadda ta ma ƙare amfani. Sannan mun sha kama kayan kwalliya na mata kamar man shafawa da man shamfo da sauransu. Abin mamakin kai da kanka ka san cewa illa ne amma wai sai ka sayar wa da al’umma a haka. Wannan al’amari akwai ban tsoro da firgici kwarai.

Ta ina ake shigo da irin waɗannan kayayyakin?
Kin san muna kusa da bodoji sannan wasu kayan daga Lagas ake taho da shi wasu daga Nijar da sauransu. Amma dai abin daɗin su shuwagabannin kasuwar nan muna aiki tare da su kuma suna ba mu ha]in kai don yanzu sai ma mu fita ka ga ba a samu kayan ba. Mutane sun fahimci abin da muke da dama ma sun daina don ma wasu da kansu suka kawo kayan don da a tunaninsu ba da gaske ake ba ko don a baya ba su ga ana aikin ba yanzu da suka ga ana yi da gasken da kansu suke kawo wa.

Wanne kira za ka yi wa al’umma kan wannan rashin amana ta wasu ‘yan kasuwa?
Ina kira ga al’umma su sani wannan hukumomin guda biyu hukumar KAROTA da CONSUMER nasu ne kuma don su aka yi kada su don haka su fito su mara ma hukumomin baya su kawo mana rahoton duk inda suka ji ko suka ga irin wannan algus ko cuta mu kuma za mu ɗau mataki.

Wanne mataki consumer suke ɗauka in an kai musu ƙorafin?
Consumer t a ce za a kai mutum kotu a hukunta shi ko kuma ya yarda cewa ya yi laifi yana so a samu daidaito ya biya tara sannan a riƙe kayan ita kuma hukuma ta sa ranar da za a ƙona kayan da kanka za ka ce kayanka marar kyau ne in kuma ba ka yarda ba a tafi kotu a yanke maka hukunci.

Akwai wasu abubuwa da ma’aikatar lafiya ce take da hurumin sani kuna tuntuɓarsu ne?
Ai ita hukumar ta ha]a da ma’aikatan lafiya da na ciniki duk a cikin hukumar suke tare ake tafiya da su. Akwai ƙwararru da quality assurance da Enforcement da ɓangaren legal da admin da education ma’ana dai kwararru ne na tabbatar da cewa abin da ake yi su kwararru ne fagensu ne suna gane kowanne al’amari.

Kwanaki da aka yi annobar ɗan tsami kun bibiya kun ji silar abin da ya janyo?
Kwarai kuwa an yi gwaje-gwaje kuma an kai wa gwamnati sakamako tana nazari kuma na tabbatar in ta kammala nazarin za ta sanarwa da al’umma me ya faru. Amma dai tuni an ɗau matakin da ya dace kuma al’umma shaida ne lokacin azumi aka fi amfani da wannan ɗan tsami amma cikin hukuncin Allah an yi azimi lafiya kuma an kammala lafiya baa bin da ya faru. Wanda hakan na cikin irin matakan da aka ɗauka na kawar da duk abin da ba shi da kyau ba ma sai ɗan tsami kawai ba.

Jaridar Manhaja tana godiya.
Ni ma na gode.