Har yanzu ƙofar tuba a buɗe ta ke – Sojoji ga ƴan bindigar Katsina

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamandan Birget na 17 na sojojin Nijeriya a Jihar Katsina, Burgediya Janar Babatunde Omopariola ya sanar da cewa har yanzu ƙofar tuba a buɗe ta ke ga ƴan bindiga da masu haddasa tashin-tashina.

Ya shawarci duk waɗanda ke cikin harkar garkuwa da mutane da su ƙaurace wa hakan ko kuma su fuskanci doka.

Burgediya Omopariola ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke miƙa wasu mutane tara da aka ceto daga hannun ƴan bindiga ga jami’an gwamnatin Katsina a Birget ɗin.

Omopariola, wanda shugaban dakarun Birget ɗin, Kanal Yakubu Nwandiscas ya wakilce shi, ya ce sojojin sun yi amfani ne da wani salo na musamman wajen ceto mutanen waɗanda aka yi garkuwa da su daga ƙananan hukumomin jihar inda aka kai su Jihar Kaduna.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan lamarin waɗanda aka ceto daga hannun ƴan bindiga da ƴan gudun hijira, Sa’idu Ɗanja ya yaba wa dukkan waɗanda suka taimaka wajen ceto mutanen.

Ya kuma bayyana yadda dakarun tsaro na haɗaka suka ceto wasu mutane 11 a ƙaramar hukumar Batsari da kuma wasu 19 a ranar Juma’a.