Har yanzu Amorim yana nazari kan karɓar tayin zama kocin Manchester United

Mai horar da ƙungiyar Sporting Lisbon, Ruben Amorim, ya bayyana cewa bai yanke shawara game da makomarsa ba, duk da sha’awar da ƙungiyar Manchester United ta nuna wajen ɗaukar sa a matsayin sabon kocinta. Sporting ta tabbatar a ranar Talata cewa United ta tuntuɓi ƙungiyar tare da bayyana shirin biyan fansar kwantiraginsa mai darajar Euro miliyan 10 (£8.3m) idan za ta ɗauke shi.

Amorim ya yi wannan bayani ne bayan nasarar da ƙungiyar Sporting ta samu kan Nacional da ci 3-1 a gasar League Cup na ƙasar Portugal a wasan kwata final a ranar Talata. A wata tattaunawa da gidan talabijin na Sport TV, Amorim ya ce, “Ban yanke wani hukunci ba tukuna. Ban san ko wannan shi ne wasan bankwana ba ko kuwa ba haka ba.”

A yayin taron manema labarai, Amorim ya ƙara da cewa: “Akwai sha’awar da Manchester United ta nuna, akwai kuma maganar fansar kwantiragi. Da zarar na sami wani abu labari daban, zan bayyana matsayina a nan. Amma har yanzu, ba ni da cikakkiyar damar yin magana sosai.”

Ya bayyana cewa zai halarci horo a ranar Laraba domin shirin wasan gasar mako mai zuwa da za su buga da Estrela da Amadora ranar Juma’a. Da aka tambaye shi ko zai kasance a wurin wasan Manchester United da Chelsea a Old Trafford a ranar Lahadi, sai ya ce: “Zan kasance a nan.” Amma da aka sake matsa masa tambayar, sai ya ƙara da cewa: ban sani ba.”