Har yanzu Amurka ba ta rabu da bukar ba

Daga IBRAHIM YAYA

A kwanakin baya ne, wasu rahotanni ke ta waɗari a kafofin sada zumunta na zamani da ma kafofin watsa labarai cewa, wai “Cutar COVID-19 ta riga ta kare a cikin Amurka”.

Sai dai tun ba a je ko’ina ba, wasu masana a Amurka suka fitar da wani bayani dake nuna cewa, ba a shawo kan cutar ba tukuna a cikin ƙasar, kuma ganganci ne da rashin hankali a rika wasa da annobar.

Abin dariya, wai yaro ya tsinci hakori.

A kwanakin nan ita ma jaridar Washington Post, da ake bugawa a ƙasar Amurka, ta wallafa wani sharhi, inda ta jaddada cewa, cutar COVID-19 ba ta ƙare ba a Amurka.

A cikin bayanin, an ce cutar COVID-19 ta daɗe tana yaɗuwa, inda wasu mutane suka mutu sanadiyar kamuwa da ƙwayar cutar, kuma cutar tana ci gaba da sauyawa, tare da mamaye duniya.

Wani sabon rahoton mako-mako game da cutar COVID-19 da cibiyar kandagarki da hana yaɗuwar cututtuka ta Amurka ta fitar, na nuna cewa, ya zuwa yanzu, matsakaicin mutane dubu 60 ne suke kamuwa da cutar a kowace rana, yayin da matsakaicin ƙaruwar mutanen da suka mutu sanadiyar cutar a kwana guda, sun kai 358.

Ban da wannan kuma, tun lokacin da cutar COVID-19 ta ɓarke a cikin Amurka, mutane fiye da miliyan 95 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da cutar ta halaka mutane fiye da miliyan 1.

Ga mai hankali, ganin waɗannan alƙaluma da masana suka zayyana, ta yaya za a ce babu wannan annoba a cikin Amurka? Ko dai lissafin Duna ne?

Don haka, ya kamata mahukuntan ƙasar Amurka su buɗe kunne da idanunsa, su kuma fahimci abubuwan dake faruwa a zahiri a cikin ƙasar game da wannan annoba, tun kafin wankin hula ya kai su dare.

Domin ikirarin da jagororin ƙasar ke yi na kawo ƙarshen wannan cuta, labarin kanzon kurege ne.

Idan kuma suka ci gaba da yaudarar kansu cewa, babu cutar a cikin ƙasar, to, duk abin da ya biyo, su ne za su yi kuka da kansu.