Har yanzu ban janye wa wani ba, inji ɗan takarar gwamnan Nasarawa a NNPP

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a inuwar Jam’iyyar NNPP, Alhaji Yakubu Maidoya ya ƙaryata jita-jitar da wasu a jihar ke yaɗawa a yanzu cewa ya janye wa gwamnan jihar wanda shine kuma ɗan takarar Jam’iyyar APC mai ci a jihar, Injiniya Abdullahi Sule.

Alhaji Yakubu Maidoya ya sanar da haka ne a jawabinsa a lokacin wata tattaunawar haɗin gwiwa da jam’iyyarsa ta NNPP da ‘yan takarar gwamnan a inuwar jam’iyyun SDP da ADC wadda suka gudanar da manema labarai a babbar sakatariyar ‘yan jarida dake Lafiya, babban birnin jihar ranar Laraba 15 ga Maris na shekarar 2023 da ake ciki.

Yakubu Maidoya ya ce ba shakka jam’iyyun suna da sanin waɗannan labaran ƙanzon kurege da wasu ke yaɗawa a jihar cewa da shi da ‘yan takarar jam’iyyun biyu (SDP da ADC) sun janye wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule.

A kan haka ne ma ya sa a cewarsa sun ga ya dace su fito fili su ƙaryata wannan labarai don wayar da kawunan al’ummar jihar da sauran magoya bayansu baki ɗaya.

Ya yi amfani da damar inda ya buƙaci al’ummar jihar baki ɗaya musamman magoya bayan jam’iyyun 3 daki-daki su yi watsi da labarin don a cewarsa babu kashin gaskiya ciki.

Ya ƙara da cewa wasu ‘yan adawa dake neman faɗuwar jam’iyyun ne suke cigaba da yaɗa labarun don tabbatar ba su yi nasara ba.

Daga nan ya sanar cewa da shi da sauran ‘yan takarar ba za su janye ba za su tsaya daram a bakan su har ranar zaɓen.

A yanzu dai binciken wakilin mu ya gano cewa a yayin da ake cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓukan gama-garin a jihar ta Nasarawa wanda ake sa ran gudanarwa a gobe Asabar 18 ga watan Maris na shekarar 2023, tuni wasu manyan jam’iyyu a jihar musamman APC dake mulki a jihar na cigaba da lallaɓar waɗannan jam’iyyun adawa musamman NNPP waɗanda suke tunanin ka iya jawo musu cikas a tafiyar don su janye wa gwamnan jihar mai ci yanzu, Injiniya Abdullahi Sule wanda ke neman zarcewa karo na biyu. Amma sai suka yi ƙememe.