Har yanzu CBN bai sakar wa INEC kuɗaɗe ba – Kwamishina

Daga BASHIR ISAH

Yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin zaɓen 2023, har yanzu Babban Bankin Nijeriya (CBN) bai sakar wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), kuɗaɗen da take buƙata domin tura kayayyakin zaɓe zuwa sassan ƙasa ba.

A makon jiya Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gana da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, inda suka tattauna yiwuwar bai INEC sabbin kuɗin da za ta yi amfani da shi wajen tura kayan zaɓe zuwa sassa.

Inda a nan Emefiele ya bai wa INEC tabbacin ba zai bari a yi wa CBN kallon ana amfani da shi wajen yi wa sha’anin zaɓe ƙafar ungulu ba.

Ya ce CBN zai bai INEC sabbin kuɗin da ytake buƙata don gudanar da ayyukanta na zaɓe.

Sai dai, alamu sun muna ya zuwa wannan lokaci INEC ba ta samu kuɗin ba kamar yadda CBN ya ba ta tabbaci, in ji Kwamishinan INEC na yankin Abuja, Alhaji Yahaya Bello.

Bello ya ce muddin aka ga wata gazawa daga ɓangaren INEC hakan ba zai rasa nasaba da sabon tsarin ‘cashless policy’ da CBN ya fitar ba.

Da yake jawabi a wajen wani taro game da sha’anin zaɓen 2023 a Abuja, Bello ya ce muddin ba a ɗauki wani matakin daƙile ƙarancin kuɗin da ake fuskanta ba, INEC a yankin Abuja za ta fuskanci cikas wajen tura ma’aikata da kayan aiki zuwa sassa yayin zaɓe mai ƙaratowa.