Har yanzu Ina nan daram a APC, inji Al-Makura

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, wanda ya fito takarar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ya ce, har yanzu yana nan a jam’iyyarsa APC daram ba gudu ba ja da baya, duk da bai yi nasarar zama shugaban jam’iyyar na ƙasa ba. 

Sanata Umaru Tanko Al-makura ya sanar da haka ne a wat takardar sanarwa na musamman ɗauke da sanya hannunsa wadda mai taimaka masa a fannin labarai, Mista Danjuma Joseph ya raba wa manema labarai a garin Lafiya, babban birnin jihar da wakilinmu ya samu kwafi. 

Ya ce jim kaɗan da rashin nasarar sa a takarar sai wasu mutane a jihar dama qasa baki ɗaya suka fara yaɗa jita-jita cewa yana shirin canja sheƙa daga jam’iyyar tasa ta APC zuwa wata jam’iyyar adawa daban sakamakon rashin nasarar. 

Sanarwar ta cigaba da bayyana cewa “akan haka ne ma ya sa nake so in yi amfani da damar nan don in ƙaryata wannan jita-jita mara tushi balle makama da wasu mahassada na a fannin siyasa ke yaɗa ta yanar gizo da sauransu cewa a yanzu Ina shirin barin jam’iyyata mai adalci (APC) sakamakon rashin nasara ta na kasancewa shugaban jam’iyyar ta ƙasa. 

Ba shakka Ina so in ƙaryata wannan labarin ƙanzon kuregen, in kuma nanata wa ɗimbin magoya bayana da ‘ya’yan jam’iyyarmu a jihar nan da ƙasa baki ɗaya cewa su yi watsi da jita-jitan su kuma sani cewa har yanzu Ina nan daram a APC ba gudu ba ja da baya,” in ji shi. 

Ya ƙara da cewa don ya bayyana wa duniya cewa ya yi na’am da zaɓin ɗan uwansa kuma abokinsa na siyasa wato sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da aka zaɓa, Sanata Abdullahi Adamu, da shi da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule tuni suka ziyarci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Abuja, inda suka nuna godiyarsu na naɗa ɗaya daga cikinsu ɗin a matsayin jim kaɗan bayan an rantsar da shi. 

Daga nan sai ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana cewa zai cigaba da bada gagarumin gudunmawa wajen cigaban jam’iyyarsa APC a jihar ta Nasarawa da ƙasa baki ɗaya kamar yadda ya saba duk da sakamakon zaɓen sabon shugaban da ya rasa. 

Jim kaɗan da bayyana Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ne maimakon shi Sanata Umaru Tanko Al-makura wanda jama’a da dama a jihar da wasu sassan ƙasar nan suka yi zaton za a bai wa muqamin sai wasu suka fara yaɗa ta kafofin sadarwa musamman ta Facebook cewa A-Makura na shirin barin jam’iyyar zuwa ta adawa sakamakon zaɓen.