Har yanzu Kannywood ba ta san ciwon kanta ba, inji Abdulkareem Muhammad

*Yadda taron Karramawa na KILAF 2021 ya gudana

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

Tsohon Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Ƙasa (MOPPAN), Alhaji Abdulkareem Mohammed, ya bayyana cewa, masana’antar shirin fim ta Kannywood har yanzu ba ta gama sanin ciwon kanta ba.

Abdulkareem ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da bajekoli da kuma karramawa na KILAF a Birnin Kano da aka kammala kwanan nan.

Taron bajekolin finafinai da karramawa mai taken “Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Fastival” wato KILAF AWARD da aka saba gudanarwa a duk shekara a bana ma an gudanar da shi a cikin watan Nuwambar da ya gabata.

A bana dai kamar shekarar da ta gabata, taron ya zamo haɗin gwiwa ne da Kamfanin da ya saba gudanar da shi ‘Moving Image’ tare da sashin koyon aikin Jarida na Jami’ar Bayero ‘Faculty of Communications Bayero University’. Kuma an gudanar da taron na tsawon wuni biyu, daga ranar Litinin 22 zuwa Talata 23 ga watan Nuwamba.

Bayan kammala taron wakilin mu ya tattauna da Abdulkareem Muhammad wanda shi ne yake shirya taron a duk shekara dangane da bambancin taron na bana da kuma waɗanda aka gudanar a baya, in da ya fara da cewar, “To shi wannan taro dai shi ne irin sa na huɗu da muka shirya, kuma abubuwa su na ta ƙara bunƙasa tun daga lokacin da aka fara shirya taron zuwa yanzu. 

Shugaban MOPPAN na Kano

“Don ka ga na biyu ya bambanta da na farko, to kuma abin da ya bambanta na uku da na biyu shi ne wannan cuta ta Korona sai ya zamo ta kawo wasu tarnaƙi na yadda mutane za su yi taro da kuma harkar tafiye-tafiye, to kuma wannan gasar dama ce da aka bayar ga duk wani mai harkar fim da harshen Afrika ya zo, don taron ya zama wani dandamali na bajekolin finafinai, a kawo masu sayen finafinai, su zo su haɗu da juna, a yi kasuwanci yadda za a samu kuɗi, kuma a ilimintar da mutane yadda suke yin shirye-shiryen finafinan su.”

Ya ci gaba da cewa, “Abubuwa da yawa da ya kamata a ce ana aiwatarwa a wannan dandamali, sai dai a cikin wannan yanayin na Korona ba zai yiwu ba, don haka sai mu ka ga maimakon mu bar taron ya kwanta har ma  ya salwanta, sai mu ka mayar da taron ya zamo ‘Conference’ yadda mutane ba sai sun zo ba za su iya halarta don haka sai ya zama ana shirya taro a gabatar da takardu, dalilin kenan da ya sa na bara da na bana abin da mu ka yi kenan, saboda haka duk sauran abubuwan da mu ka saba yi a baya, kamar shigar da fim gasa da cin abincin Afirka duk ba a yi ba.

Don haka sai aka ɗauki taken wannan taron na bana shi ne sabon yanayi da aka samu a harkar shirya finafinai. A duba waɗanne irin hayoyi ne aka bijiro da su yadda masu harkar fim za su ci gajiyar harkar fim su sayar da finafinan su a cikin wannan yanayin? 

To a kan wannan ne mu ka ɗakko masana daga ƙasashe daban daban na duniya, suka gabatar da takardun su, kuma aka tattauna, wanda kuma aka samu shigowar masana daga Ƙasar Kenya, Kamaru da Niger da kuma nan Nijeriya. “

Dangane da yadda za a yaɗa abubuwan da aka tattauna a wajen taron kuwa yadda zai yaɗu a duniya kuwa cewa ya yi, “Akwai hanyar ‘Social Media’ wadda kowa a yanzu yana maƙale da ita, sannan kuma akwai wasu hayoyi da za mu yi amfani da su kamar yadda mu ka tattara jawaban mu za mu mayar da shi littafi don masu karatu su karanta, amma waɗanda ba sa yin karatu ko me ka yi ai ba za su karanta ba, don haka za mu yi amfani da hayoyin da mu ke ganin zai isar ga masu buƙatar su yi amfani da shi. “

Dangane da nasarorin da aka samu a wajen taron kuwa cewa ya yi, “A gaskiya an samu nasarori don ka ga mun samu haɗaka da Jami’ar Bayero a wannan ɓangare na gabatar da bita, daga bara zuwa bana har illa masha Allah da su za mu rinƙa yin haɗin gwiwa. Muhimmancin wannan abin mutanen mu ba za su iya fahimta ba, amma a duniyar yanzu idan har mutum bai bijiro da hanyar isar da ra’ayin sa ga jama’a ba na yadda a ke gudanar da abubuwa, to a kwance yake.

Wasu daga cikin mahalarta taron

Don haka wannan dama ce ga ‘yan fim na Afirka da za su faɗa wa duniya yadda suke yin harkar fim, su bayyana wa duniya abin da yake damun su da kuma mafitar da mu ka samar wa kan mu. Saboda a kullum idan mu ka duba, babu wanda zai san ciwon kan sa fiye da kai, don haka wannan dama ce da mu ke so mu faɗa wa duniya cewar masu harkar fim na Afrika suna da matsalolin su, kuma sun san mafitar su, kuma wannan dandamalin abinda ya dosa Kenan.”

Daga ƙarshe ya nuna ƙalubalen sa ga masana’antar finafinai ta Kannywood da cewar, “har yanzu ba su san ciwon kan su ba, domin su duk wani taro in ba wanda za a zo a ci abinci kawai a tashi ba, to ba za a gan su a wajen ba, amma duk wata harkar da za ta bunƙasa harkar su ba za a gan su a wajen ba, kuma wannan abin kunya ne, domin duniya ta wuce a ce Jahili shi ne yake jagorantar al’umma.”