Har yanzu ta’addanci na ƙara zama barazana a Nijeriya

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kawo ƙarshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a ranar 3 ga Mayu, 2022 tare da ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa. Ya ziyarci waɗanda ta’addanci ya shafa kamar, sansanoni ’yan gudun hijira a Jihar Borno, waɗanda rikicin ta’addancin Boko Haram ya kora daga muhallan su.

Guterres ya bayyana fatansa na cewa, Nijeriya na daf da samun nasara a yaƙin Boko Haram. Ya yabawa gwamnatin Buhari bisa dabarunta da suka ƙarfafawa mayaƙan Boka Haram aqalla 37,000 kwarin gwiwar miƙa wuya tare da kai su wuraren halin gyaran hali.

Buhari ya kuma gode wa shugaban majalisar ɗinkin duniya kan rashin kyale yaƙin Rasha da Ukraine ya manta da yaqin da Nijeriya ke yi da ta’addanci. Muna kuma godiya da ziyarar Guterres da kuma ƙoƙarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi na ba da taimako ga marasa galihu, waɗanda wasunsu suka shafe shekaru 10 a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya sun haɗa kai da ayyukan agaji a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya tsawon shekaru 13 na rikicin Boko Haram. Haka kuma ta yi asarar ma’aikata da dama na cikin gida da na waje sakamakon harin ƙunar baƙin wake, da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma kisa kai tsaye.

Sai dai yadda babban mai masaukin baƙi da baƙon nasa suka yi a wajen bukukuwan, bai yi la’akari da gaskiyar cewa, yayin da ake fatan yaƙin Boko Haram ya kawo ƙarshe, an buɗe wasu sabbin iyakokin ta’addanci a wasu sassan ƙasar. Rashin tsaro da ta’addanci ke qara ta’azzara a Nijeriya. Abin mamaki ne cewa babu wani abu da ɓangarorin biyu suka yi magana game da wannan.

Wannan makauniyar ido na iya kasancewa saboda kasancewar masu ikirarin jihadi ne kawai ake kallonsu a matsayin ‘yan ta’adda. Ƙungiyoyin ta’addancin da suke aikata munanan laifuka irin na ‘yan ta’adda da kuma ‘yan ta’addar makiyaya masu ɗauke da makamai suna goyon bayansu. Har ila yau, suna kashewa, garkuwa da mutane, lalata al’umma, mayar da ‘yan asalin a matsayin ‘yan gudun hijira da kuma mamaye yankunansu.

Ko bayan da kotun da ta dace ta ayyana ‘yan bundigar Arewa maso Yamma a matsayin ’yan ta’adda, gwamnati ta kasa tura adadin da ake sa ran za ta iya murƙushe su.

Makiyaya da ke lalata Kudancin Kaduna, Binuwai, Filato, Neja da sauran sassan ƙasar nan, ba su ma cikin lissafin ta’addancin wannan gwamnati.

Dole ne mu ga duk ƙungiyoyin ta’addanci ga abin da suke kuma ba zabar zaɓi kamar yadda ake gani a yanzu ba. Ta haka ne kawai za mu iya tsara dabarun da suka dace don kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya. Abin takaici ne yadda ƙasashen duniya (UN inclusive) suke da hannu a cikin wannan zaɓe na yabon ta’addanci a Nijeriya.

Mun yi imanin cewa sabon shugabanci na gaskiya a 2023 zai yi aiki daidai gwargwado a kan duk ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya. Idan haka ta faru, muna sa ran Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen duniya za su ba da goyon bayansu gaba ɗaya don murƙushe ta’addanci a Nijeriya.

Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, Ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.