Har yanzu ‘yan Boko Haram na riƙe da Geidam

Daga UMAR M. GOMBE

Saɓanin bayanin da aka yi ta yaɗawa cewa an kashe mayaƙan Boko Haram tare da ƙwace garin Geidam daga hannunsu, wasu mazauna garin da suka buƙaci a sakaya sunansu sun tabbatar wa jaridar Neptune Prime lamarin ba haka yake ba.

Sun ce har yanzu ‘yan bindigar na riƙe da garin kuma sai ƙaruwar suke ta yi.

Wani mazaunin garin da Neptune Prime ta samu zantawa da shi da sanyin safiyar Lahadi ya ce, “Na gan su da idanuna, waɗanda suka shigo shekaranjiya suna nan, sannan sun ƙaru daga daren da ya gabata zuwa wannan safiya.”

Wani gajeren hoton bidiyo da Neptune Prime ta samu ya nuna lokacin da wasu ‘yan bindigar suka shigo garin Geidam.

Haka nan, yayin da Neptune Prime ta nemi jin ta bakin wani mazaunin garin kan batun cewa an kashe ‘yan bindigar tare da lalata motocinsu na yaƙi, sai ya kada baki ya ce, “Wannan sai dai a mafalki.”

Ya ce “Tun shekaranjiya muke ta jin cewa an fatattake su, wa ya fatattake su?

“Gaskiyar ita ce, sun zaci cewa sun shigo ne don su fasa shaguna su kwashi kayan abinci kamar yadda suka saba, shi ya sa suka gaggauta sanar da cewa sun fatattake su, sai dai wannan karon ba su bar garin ba kamar yaddda aka yi tsammani.”

Har yanzu dai ya tabbata ‘yan bindigar na nan na ci gaba da sintiri a garin Geidam inda bayanai suka nuna sun shiga raba wa jama’ar garin ‘yar takarda mai ɗauke da saƙo cikin harshen Hausa kan cewa su shigo harkar da’awarsu saboda a cewarsu suna da niyar maida garin Geidam ya zama babbar cibiyarsu.

Rahotanni daga yankin sun nuna an ga jama’a na ta ƙokarin ficewa daga garin kada ‘yan bindigar su killace su ko kuma a hallaka su yayin musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.

Sai dai duk da kasancewarsu a garin Geidam, wata majiya ta ce ‘yan bindigar ba su tsare kowa ba, haka ma babu wanda suka kashe.

A hannu guda, wani ma’aikacin gwamnati a yankin ya kira wakilin Neptune Prime a waya yana yabon sojoji bisa ƙoƙarin da ya ce sun yi.

Ya ce, “Har ga Allah sojojin sun yi bakin ƙoƙarinsu, illa iyaka suna fama da matsalar ƙarancin makamai.”

Mai maganar ya yi kira ga gwamnati da ta magance matsalar, tare da yin ƙorafin cewa Brigadier General Yerima bai yi wa mutanensu adalci ba sa’ilin da ya ce jama’arsu ba su ba su haɗin kan da suke buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *