Daga AMINA YUSUF ALI
Kwamitin mashawartan gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu sun ba shi shawarar haɗe hukumomin NIMASA, hukumar haraji (FIRS), da kuma hukumar Kwastam, dukkansu su kasance a ƙarƙashin hukumar tattara haraji ta tarayya wato FIRS.
Haɗewar a cewar kwamitin mashawartan za ta taimaka wajen amsar haraji na kai tsaye da ba na kai tsaye ba a madadin gwamnatin tarayya.
Majalisar ta nemi a yi garambawul ga dokar tattalin arziki cikin gaggawa don ba wa shugaban ƙasa damar zartar da wannan hukunci.
Wannan kwamitin mashawartan wacce Mista Tinubu ya haɗa don tallafawa wajen samar da tattalin arziki mai ɗorewa ta ƙunshi: Tokunbo Abiru (Shugaba), Yemi Cardoso, Sumaila Zubairu da Doris Anite, da kuma KPMG a matsayin waxanda za a tuntuɓa.
Kwamitin ya ba da shawarar ne a cewar so don bunƙasar haraji daga manya-manyan hukumomin tattara haraji ta yadda za a canza musu fasali don bunƙasa aikinsu na amsar haraji nan da shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa a ƙasar.
Wannan a cewarsu zai sa a kore duk wani rashin gaskiya da muna-muna da kuma tsarin binciken kuɗin.
Biyan haraji hawa-hawa ya zama wata babbar matsala a tattalin arzikin ƙasar nan.
Abinda yake hana ƙin yin biyayya ga hukumar da takure masu biyan harajin abinda yake shafar kasuwanci da gidaje ninki ba ninki.
Don warware wannan matsala, kwamitin ya bayyana muhumimmanci haɗe harajin waje ɗaya. Da kuma magance kauce wa biyan haraji.
Ta nemi a samar da kyakkyawan tsarin da zai dinga sa mutane biyan haraji da ƙashin kansu sannan kuma a samu kuɗin shiga mai yawa a gwamnatin tarayya.
Sauran shawarwarin sun haɗa da ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan tattara kuɗaɗen shiga da tsaron ƙasa, garambawul ga babban Bankin Nijeriya, CBN da sauransu.