Harajin milyan $1: Nijeriya da Ghana sun soma tattaunawa don cim ma daidaito

Daga WAKILINMU

A matsayin wani mataki na ƙoƙarin kawo ƙarshen badaƙalar harjin Dala miliyan $1 da aka ƙaƙaba wa ‘yan kasuwar Nijeriya a ƙasar Ghana, ƙasshen biyu sun soma wani zaman tattaunawa don fahimtar juna.

A Larabar da ta gabata Shugaban Majalisar Wakilai na Nijeriya, Femi Gbajabiamila da takwaransa na Ghana, Rt. Hon. Kingsford Alban Bagbin sun yi wa ‘yan majalisa bayani yayin zamansu a Abuja kan yadda Nijeriya da Gahana za su haɗa kai wajen magance matsalar kasuwanci a tsakanin ƙasashen biyu.

Bayan kammala wani taron sirri da suka yi, jagororin biyu sun shaida wa manema labarai cewa nan ba da jimawa ba matsalar cinikayya da ƙasashen biyu ke fuskanta a tsakaninsu za ta zama tarihi.

Sanarwar bayan taron nasu wadda ta samu sa hannun duka su biyun, ta nuna bayan kammala taron ne aka bai wa Shugaban Majalisar Wakilai na Ghana damar yi wa ‘yan majalisar wakilai na Nijeriya bayani.

Rashin jituwa game da sha’anin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu ya soma ne tun daga lokacin da hukumomin Ghana suka buƙaci baƙi masu kasuwanci a ƙasar su soma biyan haraji na Dala milyan ɗaya kafin su samu damar gudanar da kasuwancinsu a ƙasar.

Bagbin ya ce, “Mun samu tabbaci daga ɓangarorin biyu kan cewa wannan matsalar za ta kau ta zama tarihi. Yanzu ƙoƙari muke yi mu ga mun ɗauki matakin hana aukuwar waɗannan matsaloli a gaba.”

Tun farko a nasa jawabin, Gbajabiamila ya ce tattaunawar da suka yi ta yi nasara saboda an taɓo batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu.