Haramta kiwo a Kudu ba zai saɓu ba – Ndume

Daga UMAR M. GOMBE

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Barno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya soki matakin da gwamnonin Kudu suka ɗauka na haramta kiwo a yankinsu.

A Talatar da ta gabata ce gwamnonin suka cim ma matsayar haramta kiwo a yankinsu yayin wani taro da suka gudanar a jihar Delta.

A cewar gwammonin Kudun ɗaukar wannan mataki zai taimaka wajen daƙile matsalar rashin jituwar da ke aukuwa tsakanin manoma da makiyan yankin, sannan ya bunƙasa sha’anin tsaron yankin nasu.

Sai dai a nasa ɓangaren, sa’ilin da yake zantawa da manema labarai ya ce ɗaukar wannan mataki ba daidai ba ne don kuwa ba shi ne mafita ga matsalar ba.

Jaridar The Cable ta ruwaito saanatan na cewa, “Gwamnoni su ne shugabannin tsaron jihohinsu, don haka me ya sa gwamnonin suke maganar Shugaban Ƙasa amma ba su maganar kawunansu? Baki ɗaya gwamnonin sun saki hanya. Matsalar ba ta kiwo ba ce.

“Matsala ce ta tsaro. Galibin matsalolin da suke addabar Nijeriya ba a daji suke ba.

“Muna da matsaloli iri huɗu da suka sanya ƙasa a gaba. Ga matsalar ‘yan ta’adda a Arewa-maso-gabas, IPOB, zuwa ƙungiyoyin tsaro da aka kakkafa da suke haifar da matsalar tsaro a kudu-maso-gabas, ga kuma matsalar ‘yan fashin daji a yankin Arewa-maso-yamma.

“A shiyyar Arewa ta Tsakiya kadai muke da matsalar manoma da makiyaya. Akwai ƙarancin matsaloli a yankin Kaudu-maso-yamma, in ban da matsalar rashin jituwar makiyaya da manoma da ta masu neman kafa ƙasar Yarbawa….’

“Matsalar tsaro matsala ce da kowane yanki ke fama da ita, kuma a yanzu Shugaba Buhari ya sunkuya magance matsalar da kansa.”

Ndume ya ce afin yanzu Shugaban Ma’aikata ko Ministan Tsaro ne kan tattauna da shugabannin tsaro, amma a yau Shugaban Ƙasa ya karɓe ragamar don ganin ya shige gaba wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaron ƙasar nan.