Hare-haren Kudancin Kaduna aiki ne na rashin hankali – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi allawadai da harin da ‘yan ta’adda suka kai yankuna huɗu a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura ta Jihar Kaduna, inda suka kashe sojoji biyu da fararen hula 10, yana mai alaƙanta harin da “aiki na marasa hankali”, wanda mutum wayayye mai hankali ba zai iya aikata shi ba.

“Mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa fararen hula da jami’an tsaron da ba su ji ba su gani ba da kuma ɓarnata gidaje da shaguna abin takaici ne da allahwadai. Ƙasa gabaɗaya tana miƙa ta’aziyyarta ga jama’an Kagoro, yankin da lamarin ya faru da kuma iyalan jajurtattun sojojin da suka rasa rayukansu,” a saƙon jajentawar da Shugaban Ƙasar ya raba wa manema labarai.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa, yana tare da matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ɗauka da kuma ƙoƙarin jami’an tsaro na tabbatar da an gano waɗanda suka yi wannan ɗanyen aiki don ɗaukar matakin shari’a.

Ya kuma gargarɗi jama’a da su guje wa duk wani abu da zai kai ga ya haddasa tashin-tashina.