Hare-haren Zamfara: Mun rasa mutum fiye da 200 – Ƙungiyar mazauna Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kimanin mutane 200 ne aka kashe a hare-haren da wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, kamar yadda ƙungiyar mazauna yankin suka bayyana, biyo bayan farmakin da sojoji suka kai maɓoyar ’yan ta’addan a makon jiya.

Gwamnatin jihar ta ce, mutane 58 ne aka kashe a yawan kashe-kashen. Sai dai mazauna yankin da suka koma garuruwansu a ranar Asabar, don shirya jana’izar jama’a sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, adadin waɗanda suka mutu ya zarce 200.

Sojojin sun kai hare-hare ta sama a ranar Litinin ɗin da ta gabata a kan dajin Gusami da kuma yammacin ƙauyen Tsamre a Zamfara, inda suka kashe ’yan bindiga sama da 100 ciki har da shugabanninsu biyu.

Ƙungiyar ta ce, wasu ’yan bindiga sama da 300 a kan babura sun kai farmaki ƙauyuka takwas da ke yankin Anka a jihar Zamfara a ranar Talata inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba, inda suka kashe aƙalla mutane 30.

Haka zalika, maharan sun mamaye ƙauyuka 10 a gundumar Anka da Bukkuyum a ranar Laraba zuwa Alhamis, inda suka yi ta harbe-harbe kan mazauna garin tare da kwashe gidaje da ƙone-ƙone.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa, “an binne fiye da mutane 140 a faɗin ƙauyuka 10 kuma ana ci gaba da neman ƙarin gawarwakin saboda ba a san ko su waye ba.”

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ɗin da ta gabata, rundunar sojin ƙasar ta samu ƙarin kayan aiki domin ganowa tare da kawar da gungun masu aikata laifuka, waɗanda suka addabi jama’a cikin mu’amalar ta’addanci, ciki har da sanya haraji ba bisa ƙa’ida ba ga al’ummomin da suka yi wa ƙawanya.

“Hare-haren na baya-bayan nan a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da ‘yan fashin daji suka kai wani mataki ne na yanke ƙauna daga masu kisan kai, a halin yanzu muna fuskantar matsin lamba daga sojojinmu,” inji Buhari.

Buhari ya ƙara da cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukanta na soji domin kawar da ‘yan ƙungiyar da ke ɗauke da makamai.

Arewa maso yammacin Nijeriya dai na fuskantar ƙaruwar yawaitar sace-sacen jama’a da sauran laifuka tun daga ƙarshen shekarar 2020 a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da doka da oda.

A bara, ’yan bindiga sun yi ta yaɗa labaran duniya tare da kai hare-hare kan makarantu da kwalejoji inda suka yi garkuwa da ɗaruruwan ɗalibai. An sako yawancinsu amma har yanzu ana tsare da wasu daga cikin waɗancan ɗaliban.

Rikicin ’yan bindiga ya samo asali ne a faɗa tsakanin makiyaya da manoma da ba su da yawa a kan filaye da albarkatu. Amma hare-haren na tsawon shekaru sun zarce zuwa manyan laifuka.

Sojojin Nijeriya sun ce a makon da ya gabata sun kashe ‘yan fashin daji 537 a yankin tare da kama wasu 374 tun daga watan Mayun bara, yayin da 452 ‘yan bindiga da aka yi garkuwa da su aka ceto.

Wasu ’yan bindiga masu biyayya ga fitaccen shugaban ƙungiyar Bello Turji sun sha kashi sosai a watan da ya gabata a farmakin da sojoji suka kai ta sama da ƙasa a sansanonin su da ke dazuka.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Kabir Adamu, tare da ‘Beacon Consulting Nigeria’ da ke Abuja, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, harin na makon da ya gabata na iya zama martani ga ayyukan soji.

“Abin da ya fusata da wannan, kuma wataƙila da cewa suna fuskantar mutuwa, sai suka yanke shawarar ƙaura zuwa wasu wurare kuma a cikin haka suna kai hare-haren,” inji Adamu.

Nijeriya ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ƙungiyoyin ’yan ta’adda, wanda ke ba da damar sanya takunkumi mai tsauri a ƙarƙashin dokar hana ta’addanci ga waɗanda ake zargi da harbin bindiga, da masu ba da labari, da kuma magoya bayan waɗanda aka kama suna ba su man fetur da abinci.