Harin ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 44 a Pakistan

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga ƙasar Pakistan sun ce, aƙalla mutum 44 mutu sannan sama da 100 sun jikkata a wani mummunan hari da aka kai wajen wani taron siyasa a ƙasar.

Jami’an yankin sun ce, sun gano wasu abubuwa da ke tabbatar da cewar harin na ƙunar-baƙin-wake ne.

Harin ya auku ne a Arewa maso Yammacin gundumar Bajaur kuma a daidai lokacin da mambobin jam’iyyar Jamiat Ulema-e-Islam-Fazl (JUI-F) ke tsaka da taro.

Bayanai sun ce, an kammala aikin ceto a wurin da aka kai harin bayan da jami’ai suka samu nasarar kwashe dukkan waɗanda suka jikkata zuwa aisibiti.

Sai dai, jami’ai sun yi gargaɗin yiwuwar adadin waɗanda suka mutu sakamakon harin ya ƙaru nan gaba kasancewar mutum 15 daga cikin waɗanda suka jikkata ɗin na cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *