Harin da aka kai wa jirgin ƙasar Abuja zuwa Kaduna

Labarin da wani shaidar gani da ido kuma tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya bayar, ya nuna cewa, wasu mutane da ake kyautata zaton ’yan ta’adda ne da ke gudanar da ayyukansu a Jihar Kaduna sun zavi wani sabon salo a cikin munanan ayyukansu ta hanyar kai hari kan jirgin ƙasar Abuja zuwa Kaduna, inda yawancin matafiya ke amfani da shi don guje wa babbar hanyar titi ta Abuja zuwa Kaduna ɗin mai haɗarin gaske.

Shehu Sani ya ruwaito hare-haren sau biyu a ranakun Laraba da Alhamis a shafinsa na Facebook, inda ya ke cewa, “a jiya Laraba, ’yan bindiga sun kai hari kan jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja. Sun tayar da boma-boman da ya lalata titin dogo tare da farfasa gilashin jirgin ƙasan. Sun kuma buɗe wuta, inda suka nufi wurin direban jirgin.

“Abin ya faru ne a tsakanin tashoshin Dutse da Rijana. Direban ya yunqura ya nufi tashar Kaduna Rigasa. Da sanyin safiyar nan, Ina cikin jirgin lokacin da jirginmu ya bi ta kan layin dogon da suka lalata. Jirgin ya kusa kaucewa daga kan hanyarsa, kafin Allah ya tsirar da mu. Ya kamata a dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen ƙasa na Abuja zuwa Kaduna a yau har sai an magance wannan batu,” inji Shehu Sani.

Tashin bom ɗin da ake zargin, an ƙara tattarowa, ya yi ɓarna a cikin jirgin da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja da safiyar Alhamis, hakan ya sa aka kasa samun jirgin da zai ɗauki fasinjoji zuwa Abuja.

Majiyarmu ta bayyana cewa, a daren Laraba ne aka yi yunƙurin tayar da bom, lamarin da ya sanya jirgin ƙasan da ya taso daga Abuja karfe 6:40 na yammacin Laraba ya isa Kaduna da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren Alhamis.

Jirgin na yammacin Laraba ana sa ran isowarsa Kaduna da ƙarfe 8:40 na dare, amma saboda ya ɗauki sa’o’i da dama da jami’an tsaro suka yi wajen kawar da hatsarin, jirgin ya kwashe sama da sa’o’i takwas a tafiyar sa’o’i biyu da ya saba.

Wannan lamari dai na zuwa ne makonni kaɗan bayan wani bayanan sirri da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP sun yi na tserewa daga dajin Sambisa zuwa dajin Rijana da ke Ƙaramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, tun a ranar Talatar makon da ya gabata ne hukumomin tsaro a Jihar suka fara fafutukar ganin sun daƙile harin da ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan ƙungiyar ISWAP da Boko Haram ne suka kai wa jirgin.

A cewar majiyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, “’yan ƙungiyar ISWAP da Boko Haram sun shiga Kaduna, amma jami’an tsaro sun yi ta ƙoƙarin hana su kafa sansaninsu a kowane yanki na Jihar. Ranar Talata har zuwa safiyar Laraba, ba mu iya yin barci ba saboda muna fafutukar ganin mun fatattaki ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin tayar da bam a wata gadar da jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ke amfani da shi”.

Sai dai hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC), ta musanta rahotannin da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna KA4 tsakanin Asham da Kubwa hari. Manajan Daraktan NRC, Fidet Okhiria, wanda ya musanta hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce, rahotannin ƙarya ne.

A cewarsa, a kodayaushe akwai ’yan iska da ke jifan jirgin da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

“Babu wani harin ’yan bindiga a cikin jirgin, jita-jita ce kawai in ba haka ba ai da za su ga harsashi a cikin jirgin. ’Yan iska ne suka yi jifa da duwatsu a jirgin kuma saboda ‘yan sanda sun samu mutum ƙaya da ake zargi, da daddare wasu ‘yan daba suka fito suka far wa jirgin domin nuna adawa da kama ɗayansu da aka yi da rana. Duk da haka, NRC ta yi magana da jami’an tsaro da su taimaka mana wajen hana afkuwar irin haka nan gaba tare da tsoma baki cikin lamarin, don haka za su san yadda za a shawo kan lamarin,” inji Okhiria.

Ya buƙaci jama’a masu amfani da jiragen ƙasa da kada su firgita domin Ministan Sufuri da NRC za su tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya a kan wannan hanya.

Haka zalika, Manajan Sashin Jirgin Ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, Paschal Nnorli, ya tabbatar da cewa jirgin ya isa tashar Idu a ranar Litinin, kuma ya musanta harin da ’yan bindiga suka kai.

Nnorli ya ce, “an jawo hankalin kamfanin jiragen ƙasa na Nijeriya kan labaran ƙarya na yanar gizo cewa wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kai wa jirgin KA4 da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja hari a ranar Litinin da ta gabata a tsakanin Asham da Kubwa. Bayan harin, Hukumar Kula da Jiragen Qasa ta Nijeriya (NRC) ta dakatar da ayyukan jirgin ƙasa da ba a sani ba a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Fasinjojin da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja sun koma babban birnin ƙasar bayan jinkirin da ya ɗauki aƙalla sa’o’i biyu. Sai dai Hukumar NRC ta sanar da buɗe hanyar Abuja zuwa Kaduna kwanaki biyu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai wa wani jirgin ƙasa hari.

Hare-haren da aka kai tsakanin yammacin Laraba zuwa safiyar Alhamis sun kuma lalata wasu sassan titin jirgin. Sanarwar da NRC ta sake buɗewa a yammacin ranar Juma’a, ta ce, “Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC) suna sanar da jama’a, musamman ma fasinjojinmu cewa jirgin Abuja zuwa Kaduna na AKTS za su koma gobe Asabar 23 ga Oktoba 2021, kamar haka: daga, IDU, Abuja (AK3) da ƙarfe 0950 na safe, daga Rigasa, Kaduna (KA4) da ƙarfe 1035 na safe. Ayyukan jiragen ƙasan za su ci gaba da aiki, kuma ta sake ba da haƙuri da gaske kan abin da ya faru.”

Ko ta yaya, harin da aka kai kan jirgin ƙasar Abuja zuwa Kaduna, abu ne da ya kamata ya damu duk wani ɗan ƙasa mai hankali, musamman waɗanda ke da haƙƙin samar da tsaro ga jama’a. Rashin tsaro da ya shafi garkuwa da mutane, ‘yan fashin daji, fashi da makami, tayar da ƙayar baya da kuma fyaɗe ya tilasta wa matafiya da yawa ciki har da manyan mutane yin amfani da jirgin ƙasa a matsayin aminci.

Bisa ga wannan gaskiyar ne muke kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi ta hanyar tabbatar da cewa tsarin sufurin jiragen ƙasa ya kasance lafiya, musamman ga talakawan Nijeriya da ba za su iya biyan kuɗin jirgi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *