Harin Filato: Sufeto-Janar ya ba da umarnin tura rundunar bincike, an damƙe mutum 20 an ceto 33 – Mba

Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin gaggawa da a tura rundunar bincike zuwa jihar Filato domin auna ɓarnar da ta auku yayin harin baya-bayan nan da kuma saka ƙaimi wajen ci gaba da tabbatar da lumana a yankunan da lamarin ya shafa.

Baba ya ba da wannan umarnin ne cikin wata sanarwar manema labarai da ta fito ta hannu mai magana da yawun rundunar na ƙasa, CP Frank Mba, ran Lahadi a Abuja.

Sanarwar ta ce ɗaukar matakin tura rundunar ya faru ne sakamakon harin da aka kai wa mazauna yankin Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, wanda ya auku a Asabar, 14 ga Agustan 2021.

An tura tawagar ne ƙarƙashin jagorancin DIG Sanusi N. Lemu, wadda ta ƙunshi jami’ai daga sassa daban-daban na rundunar inda za su yi binciken gano waɗanda ke da alhakin harin tare da hana aukuwar haka a gaba.

Baya ga Allah-wadai da harin da IGP Baba ya yi, ya kuma yi kira da a zauna da juna lafiya, tare da bai wa al’ummar da rikicin ya shafa tabbacin jami’an za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen bankaɗo waɗanda ke da hannu a badaƙalar don su fuskanci hukunci.

Ya ce kawo yanzu, an kama wasu mutum 20 da ake zargi suna da hannu a harin, sannan an ceto mutum 33.

Daga nan, Baba ya buƙaci al’ummar yankin da su bai wa jami’an tsaron da ke aiki a yankin haɗin kai ta hanyar taimaka musi da muhimman bayanan da suka dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *