Harin jirgin ƙasa: ’Yan bindiga na barazanar kashe fansinjojin da suka sace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindigan da suka dasa bam a hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, su ka yi awon-gaba da bayin Allah su na barazanar cewa za su kashe mutanen da ke hannunsu. 

Jaridar Daily Nigerian ta fitar da faifan bidiyon ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da Manajan Darakta na Bankin Manoma a Nijeriya, Alwan Hassan, ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu 2022, inda aka ji cewa waɗannan ‘yan ta’addan su na gargaɗin gwamnatin tarayya a lokacin da suka ce za su saki Alwan Hassan ya koma ga iyalansa.

A wani gajeren faifen bidiyo da ya bayyana a ranar Larabar, an ji ‘yan bindigan su na cewa ba kuɗi ne a gabansu ba. Akasin yadda aka saba ji idan an ɗauke mutane. 

 Kamar yadda suka bayyana, waɗannan ‘yan bindiga sun ce gwamnati ta san abin da suke nema. Alwan Hassan ya kubuta.

“Mu ne gungun waɗanda mu ka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa kwanakin baya. Daga ciki har da wannan mutumi da ya roƙi mu kyale shi saboda shekarunsa.

“Sai mu ka ji tausayinsa, ganin cewa watan Ramadan ya zo, za mu so mu miƙa shi ga iyalinsa,” cewar ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan.

Waɗannan ‘yan ta’adda sun ja kunnen gwamnati da cewa ka da ta ruɗu ganin an saki wannan bawan Allah, domin sun yi hakan ne kurum la’akari da tsufansa. 

“Kashe su ba wani wahala ba ne a wajen mu,” cewar ‘yan bindigar.

“Ina so in jaddada cewa abin da ya faɗa gaskiya ne. Ka da ku nemi bincikenmu, ko ƙoƙarin ceto su domin hallaka su ba wani abu ne mai wahala a wajen mu ba.

“Ba mu son kuɗinku, da kuɗi muke nema, da ba mu kai harin ba. Kun san abin da mu ke buƙata,” cewar ‘yan ta’addar.