Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: Mahara sun sako mai juna-biyu

Daga BASHIR ISAH

‘yan bindiga sun sako wata mata mai juna-biyu tare da wasu daga mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna wanda ya auku lokutana baya.

Manhaja ta gano cewa maharan sun sako matar ne bisa ganin damarsu.

Hoton bidiyon matar da lamarin ya shafa ya yi ta karakaina a soshiyal midiya inda aka ga matar sanye baƙin hijabi da baƙin abin rufe baki da hanci. Tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da daidaita da maharan domin a sakon ragowar mutanen da ke hannunsu.

Ta ce lamarin abin damuwa ne matuƙa saboda rashin tabbas kan yiwuwar kubutar da sauran mutane da ake tsare da su.

Haka nan, matar ce ‘yan bindigar suna ba su kyakkyawar kulawa suna ciyar da su yadda ya kamata da kuma kula da lafiyarsu.

Manhaja ta tuna cewa an yi garkuwa da matar tare da sauran waɗanda lamarin ya hafa ne a ranar 28 ga Maris, 2022.