Harin Yauri: An kuɓutar da malamai 2, ɗalibai 6

Daga AMINA YUSUF ALI

Alamu sun nuna malamai biyu da kuma ɗalibai shida na Federal Government College (FGC) Yauri da aka yi garkuwa da su, sun kuɓuta.

Bayanai sun tabbatar da cewa an samu nasarar kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa ne sakamakon kwanton ɓaunan da da jami’an tsaro suka yi wa ‘yan bindigar da suka kai wa makarantar hari.

Tun bayan aukuwar harin da aka kai FGC Yauri sama da sa’o’i 24 da suka gabata, har yanzu babu wani bayani da aka fitar a hukumance kan batun, walau daga gwamnatin jihar Kebbi ko ‘yan sanda.

Ɗalibai kimanin su talatin haɗa da mataimakin shugaban makarantar ne aka ce sun ɓace sakamakon harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *