Harin NDA: Manjo Datong ya samu kuɓuta daga hannun masu garkuwa

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai Sojan nan mai muƙamin Manjo wato Manjo DL Talong wanda masu garkuwa suka sace a makarantar horas da sojoji ta NDA ya samu kuɓuta daga hannun masu satar mutane.

Shi dai sojan an sace shi ne sakamakon wani hari da masu garkuwa da mutane suka kai makarantar horas da sojojin wacce take kaduna a ranar 24 ga watan Agustan da ya gabata.

Inda a sakamakon harin ma har wasu manyan jami’an sojoji suka rasa rayukansu. Sai kuma a daren juma’ar ne nan da ta gabata ne, aka samu labarin cewa, Datong ya kuɓuta. Kamar yadda mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin Najeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya tabbatar da lamarin na cewa, rundunar sojojin ne suka kuɓutar da Manjon.

Inda ya ƙara da cewa, Sun yi nasarar kuɓutar da shi bayan sun bankaɗo kuma sun yi fata-fata da wasu maɓoyan ɓata-gari da dama da suke a garin Afaka, Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Inda ya ce hukumar sojin sun haɗa kai da rundunar sojojin sama, da sauran jami’an tsaro inda suka jajirce suka yaƙe su. Har ma suka samu nasara a kan ɓata-gari a daren juma’ar. Inda daga bisani har suka gano wani sansani inda ake zargin ana tsare da Manjo Datong. Inda a nan ma sai da suka yi musayar wuta da ɓata-garin kafin su ƙwato shi.

Rahotanni sun bayyana cewar, Manjo Datong yana cikin ƙoshin lafiya sai dai wasu raunuka da ya samu. Inda aka kai shi asibiti aka yi masa magani, sannan aka miƙa shi ga NDA.

Daga ƙarshe Ezindu Idimah, ya yaba wa jami’an sojoin sama, da na DSS da kuma ‘yansanda a kan ƙoƙarinsu wajen kuɓutar da Datong. Inda ya kwatanta su da masu kishin nasa. Sannan kuma ya ce tsugunno har yanzu bai ƙare ba, har sai an gano mutanen da suka kashe sauran sojojin guda biyu, kuma an yi musu hukunci.