Harin sojoji ya sake sanadin mutuwar mutane 16 da ƴan bijilante a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Asabar ne wani abin alhini ya sake faruwa a ƙauyen Tungar Kara da ke gundumar Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara bayan wani ruwan wuta na rundunar sojojin sama ya yi kuskuren kashe fararen hula da wasu jami’an sa kai na ZCPG.

Aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu a yayin al’amarin.

Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya auku ne jim-kaɗan bayan ƴan bindiga sun kai hari a yankin sun tsere.

Ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar mazaɓar Maradun II, Maharazu Salisu Gado Faru ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana hakan a matsayin hatsari da ya afka wa jami’an sa kan a lokacin da suka shirya fuskantar ƴan ta’addar.

Ya ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba.

Haka kuma rundunar sojoji ba ta kai ga fitar da saƙo na musamman game da lamarin ba.

A safiyar ranar Lahadi ne rundunar sojojin sama ta fitar da sanarwar nasarar harin da ta kai a maɓoyar jagoran ƴan bindiga, Bello Turji inda ta kashe da dama daga cikin kwamandojin dabarsa.