Harin Tudun Biri: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 126

*Sau biyu sojoji na jefa mana bom, in ji wasu da suka tsira

Daga BASHIR ISAH

Kawo yanzu, adadin waɗanda suka mutu a harin kuskuren da sojoji suka kai Tudun Biri, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna, ya kai 126.

An tabbatar da hakan ne a lokacin da jami’an ƙungiyar Amnesty International suka ziyarci waɗanda harin ya shafa a ranar Talata.

Wasu da suka tsira daga harin sun bayyana cewa, sau biyu sojojin na jefa musu bom.

A ranar Lahadin da ta gabata wani harin bom da sujoji suka yi nufin kaiwa a kan ‘yan ta’adda ya kuskure ya faɗa a kan taron jama’ar da ke gudanar da bikin maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke yankin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.

Tuni dai Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki alhakin kai harin, inda Hukumar Bada Agajin Gaggawa, NEMA, ta faɗa a ranar Litinin cewa mutum 86 ne suka rasa rayukansu, sannan 66 sun tagayyara a iftila’in.

Wannan mummunan al’amari na ci gaba da shan suka musamman daga Arewacin Nijeriya, inda ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da dama ke kira kan a binciko waɗanda ke da hannu a lamarin don su fuskanci hukunci.