Harin Tudun Biri: Matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna ɓacin rai a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Wasu mata a garin Zariya, Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna ɓacin ransu dangane da harin soji da ya faɗa kan masu maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a jihar.

An ga masu zanga-zangar sun yi tattaki a cikin garin na Zaria ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kamar; “Adalci ga Arewa”, “Adalci ga Igabi” da sauransu.

Sama da mutum 80 ne suka mutu sannan wasu da dama sun tagayyara sakamakon harin da sojoji suka jefa bom har sau biyu ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuƙi a kan jama’ar da ke taron bikin maulidi a ranar Lahadin da ta gabata da daddare.

Wannan na ɗaya daga cikin hari mafi muni a tarihin Nijeriya wanda aka yi kuskuren kaiwa kan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba.

Wasu da suka tsallake rijiya da baya a harin sun ce sau biyu sojoji na jefa bom ɗin, yayin da Rundunar Soji ta ɗauki alhakin kai harin, sannan jami’an ƙungiyar Amnesty International da suka ziyarci wurin da lamarin ya faru sun tabbatar da ana samun ƙaruwar waɗanda suka mutu.