Harin ‘yan bindiga: Fursunoni 240 sun tsere daga gidan yarin Kogi

Bayanai daga Jihar Kogi na nuni da cewa, aƙalla fursunoni 240 ne suka tsere sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a matsakaicin gidan yarin da ke Kabba a jihar.

Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari na ƙasa, Mr Francis Enobore, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ran Litinin, inda ya ce an kai harin ne da tsakar daren Lahadin da ta gabata.

A cewar jami’in, ‘yan bindigar waɗanda ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari gidan yarin ne ɗauke da manyan makamai wanda ya kai ga an yi musayar wuta da masu gadin gidan.

Ya ci gaba da cewa, Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yari na Ƙasa, Haliru Nababa, ya bada umarnin samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen kamo fursunonin da suka arce yayin harin, tare da gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.

Haka nan, Nababa ya yi kira ga al’ummar yankin da lamarin ya auku da su taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanan da za su taimaka musu wajen damƙo fursunonin da suka gudu.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna an gina gidan yarin Kabba ne a 2008 wanda ke da girman ɗaukar fursunoni 200.

Kuma ya zuwa faruwar wannan hari, baki ɗaya fursunoni 294 ne ake tsare da su a gidan wanda daga ciki, mutum 224 na zaman jiran shari’a ne sannan 70 daga ciki an yanke musu hukunci.