Harin Yauri: An ceto ƙarin malami ɗaya, ɗalibai uku

Daga AISHA ASAS

Sojojin Nijeriya ƙarƙashin shirin Operation HADARIN DAJI tare da taimakon sojojin sama, sun yi nasarar ceto ƙarin waɗanda aka yi garkuwa da da su a FGC Birnin Yawuri.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna waɗanda aka kuɓutar ɗin sun haɗa da malami ɗaya da ɗalibai uku, an kuɓutar da su ne a Makuku.

Sanarwar da ta fito daga Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na Sojojin Nijeriya, Brigadier General Onyema Nwachukwu, ta nuna baya ga kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa, haka nan jami’an sun kashe ɗaya daga cikin ɓarayin sannan sun ƙwato babura guda tara daga wajen ɓatagarin.

Sanarwar ta ce an tura ƙarin dakaru zuwa dajin da ɓarayin suka ɓoye a ciki domin hana su kataɓus.

Idan dai za a iya tunawa, a Juma’ar da ta gabata jami’an tsaro suka kuɓutar da malamai biyu da ɗalibai biyar daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *