Harkar fim kasuwanci ne mai kyau ga wanda ya ɗauke ta hakan – Faruƙ Gwammaja 

Faruk Gwammaja wanda ke riƙe da muƙamin ma’aji a ƙungiyar sakatarori ma’aikatan jami’o’i reshen jami’ar Bayero ta Kano.

Ya bayyana wa Blueprint Manhaja ƙudirinsa na son taimaka wa al’umma, wanda hakan zai ci gaba koda bayan ransa.

A tattaunawar sa da wakiliyarmu Bishira Nakura, za ku ji batutuwa da nake da tabbacin zai amfane masu karatu, don haka ku biyo mu don jin yadda hirar ta kaya;

MANHAJA: Mai karatu zai ji daɗi idan ka faɗa mana cikakken sunan ka da sunan da aka fi saninka da shi, sannan da tarihinka a taƙaice.

FARUK: Umar Muhammad Abdullahi, ana kira na da Farouƙ Malam Muhammad Gwammaja, an haife ni sama da shekaru arba’in da suka wuce a Gwammaja da ke ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kanon Najeriya. Na fara karatun Allo a gidanmu, daga baya aka kai mu makarantar Alkur’ani ta Gwani ɗanzarga da ke unguwar Koki, inda na yi firamare da sakandare a can, na samu gurbin karatu a Jami’ar Bayero inda na karanci fannin Larabci/Hausa/Nazarin Addinin Musulunci, na yi difiloma a Fasahar Sadarwa (Diploma in Information Technology) a HIIT-Kano, kuma na karanci Fasahar Gudanar Aikin Ofis (Office Technology and Management) a Makarantar Polytechnic ta Kano, a yanzu haka ina aiki a Jami’ar Bayero ta Kano. Ni ne Ma’ajin Kungiyar Sakatarori Ma’aikatan Jami’o’i, (Uniɓersity Secretarial Staff Association – BUK Branch) reshen Jami’ar Bayero ta Kano.

Ina cikin ƙungiyoyi da dama na taimakon al’umma, daga cikin su akwai, Gidauniyar Taimako da agaji ta Nakura (Nakura Charity Trust Foundation) da ƙungiyar masu shirya wasan-kwaikwayo (Dabo Film Production Association), Kano, ƙungiyoyin wayar da kai da tsaro da aikin gayya da dai sauransu,

Kana sana’a ne ko aikin gwamnati?

 Na yi sana’o’i kala-kala, amma yanzu na tsaya a sana’ar ɗab’i (Printing), ni ne ma Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar Masu ɗab’i ta Jalla ta Jihar Kano, (Jalla Printers Association).

Kana da aure inkada yayanka nawa?

Ina da aure da ‘ya’ya uku, rayayyu.

Ko zaka iya faɗamana irin gwagwarmayar rayuwar da ka sha?

Gwagwarmayar rayuwa har yanzu ana kanta tun daga yarinta, na yi karatun allo, har bara na ɗanyi, (duk da a gari nake), na yi islamiyya da boko daidai gwargwado, na fara koyon sana’o’i da dama irin su kafinta da ɗaukar hoto da gyaran radiyo da talabijin da sayar da agogo, sarƙa da ɗan-kunnai, da jari-bola da ci-ko-tsaraba (biskit da alewa a tasha), na yi gyaran kwamfiyuta.

A ɓangaren aiki kuma, na yi koyarwa a wasu makarantu (sai dai ban daɗe ba), na koyar da lissafi (Maths) da Ilimin Kwamfiyuta da wata makarantar kuma ƙur’ani da Larabci da turanci.

A ɓangaren ƙungiyoyi kuma na yi su yawa, wasu ba zan iya tuna su ba, daga ciki akwai irinsu, Majalisar Masoya ta Bunun Sharada Alh. Nura Ahmad (Nuran Masoya) shi da Alh. Ado Ahmad Gidandabino MON (Sarkin Marubutan Hausa na Afirka), Sai Burin Zuciya ta Jaridar Leadership Hausa, sai Gizago da Dodorido ta Jaridar Aminiya, Gidauniyar Tallafawa Marayu ta Haj. Bushra Aminu Nakura da ƙungiyar wasan kwaikwayo ta Dabo (Dabo Film Production/Association) hakan ta sa har an ɗan fara sani a wasu finafinai.

Mu ɗauki sana’arka ta ɗab’i wato printing. Ko wacce irin gudunmawar kake bayarwa ga wannan sana’a taka?

A matsayi na jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar masu ɗab’i ta Jalla Kano, na kan yi ƙoƙari daidai iyawa ta wajen faɗakarwa da wayar da kan ‘yan uwa da na ga suna buga wasu takardu da ba su dace ba, irin masu ɗauke da batsa da kuma gyare-gyaren da suka shafi yaren Hausa ko Larabci ko turanci. A ƙungiyance akan yi ƙoƙarin ganin an tsaftace harkar daga lalacewa.

Ta ya kake iya gudanar da dukkan ayyukanka ba tare da wani ya shiga cikin wani ba?

Gaskiya kowane aiki yana da nasa lokacin, misalin sana’ar ɗab’i da na ce, bayan mun tashi daga ofis ko ranakun da babu aiki nake zuwa na gudanar da ita, sai in har ta zama ta gaggawa, na ka nemi izinin na gaba dani na fita na yi, wanda kuma ba sai na fita ba, daga nan zan kira waya ayi min, haka yake a sauran ɓangarorin, irin fim.

Meye ya ja hankalin ka ka shiga ƙungiyoyi da yawa haka?

Shiga ƙungiyoyi na ya faro asali tun daga sakandare da nake ƙungiyar ɗalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN), fitar da muke yi wurare ya sa na fara sabo da jama’a, sai suka riƙa gayyata ta zuwa tarukan wasu ƙunyoyin, irin su na marubuta (ANA) daga nan na ji ni ma ina sha’awar bada tawa gudunmawar cikin harkar ƙungiyoyi, Allah da ikon sa, wasu da na je ake ganin ya kamata a bani muƙami ko a nuna ana so na zama mamba na kusa-kusa, na kan ƙoƙarta wajen ganin na bada tawa gudunmawar ko da da shawara ce.

Waɗanne irin ayyuka kuke gudanar wa?

Yawancin ayyukan ai sun ta’allaƙa ne ga rayuwar al’umma, wajen faɗakarwa da wayarwa da kawo musu cigaba da taimakonsu, waɗannan su ne wasu daga cikin ayyukan da muke gudanarwa a ƙungiya.

Me ka fahimta game da harkar fim?

Abinda na fahimta da harkar fim shi ne, harka ce kuma kasuwanci ne mai kyau, amma ga wanda ya ɗauke shi a hakan, kamar yadda kowane kasuwanci yake, akwai na gari akwai ɓata gari, duk da niyyar da mutum ya shiga a haka zai ganta. Fatana a riƙa samun waɗanda suke ganin ba a aikin kirki a ciki su riƙa shiga don su kawo gyara, amma muna gefe ba za mu hangi matsala sosai ba sai abinda wani ya je sau ɗaya ya ni ya bamu labari. Harkar fim dai da yaren na Hausa ake yi, duk mai kishin yaren zai iya shiga don ya taimaka, idan ka ƙi ko kin ƙi sai wasu ƙabilun da suka iya Hausa su shigo, daga nan su riƙa shigar muku da al’adunsu, kuna kallo kuna zagi, ‘ya’yanku suna kwaikwayo. Allah Ya kyauta.

ƙasashe nawa ka taɓa zuwa?

Ban taɓa zuwa wasu ƙasashe ba.

Jahohi nawa ka taɓa ziyar ta?

Jihohi da na je sunkai goma sha biyar (15) waɗanda zan iya tunawa.

Ko akwai ƙasar da kake son zuwa idan hali ya samu?

ƙarai akwai ƙasashen da nake son zuwa Afrika da ƙasashen larabawa da Turai, kamar Habasha, Kamaru, Ghana, Saudia Dubai, Misra da sauransu .

Yaya kake kallon rayuwar da da ta yanzu?

Rayuwar da da ta yanzu akwai bambance-bambance masu tarin yawa, a ƙarancin shekaru irin namu, mun san a wancan lokacin akwai taimakon juna, wanda mutune ba sa tsoron talauci, da girmama na gaba ko da ba a san shi ba, wanda an samu ƙarancin haka a yanzu, tarbiyya da ƙunya ga mata sun ƙaranta, wasu suna da kuɗaɗen da iyayen su ba su taɓa mallaka ba, amma ba zai iya kwatanta irin taimakon iyayensu suke yi ba, da dai tarin abubuwa da lokaci ba zai bari na kawo su ba.

Ko kana da wani buri da kake son cikawa ?

ɗan adam ai ba a raba shi da buri, akwai rututu, har burin buɗe wuraren sana’a nake da zan ɗan samawa ‘yan uwa abin yi.

Burin da nake son cikawa shi ne, samar da wata hanya da al’umma za su yi amfana da ita ko bana raye.

Wacce shawara zaka bai wa mutane da shugabanni?

Shawara ta al’umma ita ce, mu yi ƙoƙari mu riƙa kamanta gaskiya a duk al’amuran mu da yiwa junanmu kyakkyawan zato, da rage fushi da yawan addu’a. Shugabanni kuma su ji tsoron Allah su kyautatawa wa al’ummar su, zalunci baya ɗorewa, adalci ne ke wanzuwa kuma a ga rubarsa duniya da lahira.

Wane abu ne na farin ciki wanda ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Abubuwan farin ciki da ba zan manta da su ba suna da yawa suma, akwai mata da nake tunawa, tun ina ƙarami, takan shafa kaina ta bani Kwabo, saboda an ce ni maraya ne, sun daɗe suna nemarwa ɗanta gurbin karatu ba su samu ba, sai Allah Ya ƙaddara ta ɓangare na za a samu, ta yi farin ciki sosai, har ta ce wai nawa za ta biya ni? Na bata labarin irin abin ta yi min yarinta, ita ma ta manta.

Wane abu ne na baƙin ciki wanda bazaka taɓa mantawa da shi ba?

Abubuwan baƙin ciki suna da yawa, rasuwar yayata da ƙannina, da satar abin hawa da aka yi min, makon da na siya makon a ka sace.

Meye yake baka tsoro a rayuwa?

Ba zan iya cewa ga abin da yake bani tsoro a yanzu ba har sai idan ya zo.

Me ka fi so ayima kyauta da shi?

Bani da zaɓi a kyauta, duk abinda aka bani na kan yi matuƙar farin ciki, kuma bana mantawa.

Wane abu ne yake saurin saka ka jin haushi?

Abinda ke ba ni haushi shi ne a rena min hankali.

Wane kalar abinci da abin sha ka fi so?

Abinci ban fiye zaɓi ba, duk abinda ya samu zan ci, amma ina son shayi ba madara mai zafi.

Yanayin gari wanne ka fi so damina sanyi da zafi?

Ina son yanayin damina.

Meye burunka wanda kake son cikawa?

Burin da nake son cikawa shi ne, samar da wata hanya da al’umma za su amfana da ita ko bana raye.

Meye kake so ga mutane?

Ina son in yi kira ga ‘yan uwa da su ƙoƙarta wajen ƙirƙirarwa ‘ya’yansu kawunan wajen neman sana’a, duk ƙanƙantar ta, kar mu dogara da dole sai aikin gwamnati, masu aikin ma wasu da na sani suke yi, na rashin sana’a. Waɗanda suke ganin ‘ya’yan wasu a matsayin marasa tarbiyya su yi ƙoƙari wajen ganin yaya za a samu su gyaru, ta ɓangaren taimaka musu da ba su shawarwari, sai kana ɗan bada gudunmawa za a fi jin nasihar ka da faɗanka.

Su waye gwanayen ka a duniya ?

Gwanayena na kusa da ni dai akwai su Farfesa Sani Muhammad Gumel, Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, da Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Suke ta Kano da Alh. Ado Ahmad Gidandabino MON, Sarkin Marubutan Hausa na Afirka da Alh. Balarabe Abdullahi Wayya da wasu ma da dama.

Ko kana da wanda za ka gaisar?

Ina da waɗanda zan gaisar sosai ma, ina gaishe da ‘yan uwa da abokan arziki da abokan aiki da abokan kasuwancin da na siyasa da na makaranta, da Haj. Bushra Aminu Nakura shugabar mu ta Nakura Charity Trust Foundation da Alh. Aliyu Dangida da Mal. Abdurrahman Dodo.

Fatan ka ga jaridar Blueprint Manhaja?

Zan yi godiya ga jaridar Blueprint Manhaja bisa irin faɗakarwa da wayar da kan al’umma da suke yi, tun kafin wannan jarida da kuma gode musu bisa wannan hira da suka yi da ni. Allah Ya ƙara ɗaukaka su ya yi musu jagoranci.