Harshe na asali yana da daraja matuƙa

Sharhi daga BELLO WANG

Yau rana ce ta harshe na asali, wadda hukumar UNESCO ta keɓe don tunatar da al’ummun duniya muhimmancin kare yarensu na asali.

Dalilin da ya sa harshe na asali ke da muhimmanci, shi ne yana da amfani wajen bambanta mu da sauran al’ummomi. Saboda haka, harshenmu na asali tamkar lu’u-lu’u ne da aka gaje su daga magabantanmu. Sai dai wasu daga cikin “lu’u-lu’un” sun riga sun ɓace. Yau na karanta wani labari dake cewa: wata mace mai suna Cristina Calderon ta rasu a kwanakin baya, tana da shekaru 93 a duniya, da rasuwar ta kuma an rasa mutum ta ƙarshe tsakanin dukkan mutanen duniya, wadda ta iya yaren Yamana, wani harshe na ‘yan ƙabilar Yagan a ƙasar Chile. Ko da yake ana ci gaba da samun wasu mutane fiye da goma, wadanda suke kiran kansu da ‘yan ƙabilar Yagan, amma tun tuni sun daina koyon harshen wannan ƙabila wato harshen Yamana, da magana da shi. Saboda haka, wannan yare shi ma ya mutu yanzu.

Bisa alƙaluman da MDD ta samar, an ce aƙalla kashi 43% cikin dukkan harsuna kimanin 6000 da ake samu a duniyarmu, suna bakin mutuwa. Cikin sauran harsuna, wasu fiye da dari ɗaya ne kawai ke taka muhimmiyar rawa a fannonin aikin ilmantarwa, da mu’ammalar jama’a. Idan ana son ƙirga harsunan da ake iya buga su da na’urar kwamfuta, da rubuta bayanai da su a shafukan yanar gizo ta Internet, to, ba za su wuce ɗari ɗaya ba.

Wasu dalilai da yawa sun sa harsuna na asali fadawa cikin mawuyacin hali: Misali, wasu al’adu na yaɗuwa a duniya, lamarin da ya sa ake ƙara yin amfani da yaren dake tare da al’adun, wanda ya ƙunshi fina-finai na Hollywood, da waƙoƙi na Turanci masu farin jini, da makamantansu. Ban da wannan kuma, wayar salula ta zamani, da manhajar sadarwa sun sa muke kara fada wa juna magana, maimakon rubuta wasu saƙonni, ta yadda mu kan manta da rubutaccen harshe. Haka zalika, kalmomi na harsunan waje, da maganganun da ba su yi daidai ba, sun cika shafukan Internet, wannan batu ya ƙara matsalar rashin yunkurin daidaita harshe, da koyar da shi ga dalibai, sun sa an shiga wani yanayi na fama da rikici a fannin yin amfani da yaren, abun da ke ba mutane wahala lokacin da suke son magana da juna, ta yadda sannu a hankali, ake fara yin amfani da harsunan ƙetare maimakon na asali.

Saboda haka, muna samun waƙoƙi, da wasannin kwaikwayo, da sauran al’adun gargajiya, waɗanda da akwai, amma yanzu babu, a wasu wurare daban daban. A wasu ƙasashe, idan wani mutum na son neman wani littafin da aka rubuta da yaren ƙasar na asali, game da tarihi na ƙasar, ba zai samu ba, illa dai littattafan da mutane na sauran ƙasashe suka rubuta kan tarihin ƙasar. Wataƙila akwai ƙarairayi a cikin waɗannan littattafai, amma mutum ba shi da sauran zaɓi. Kana wani abun da ya fi janyo damuwa shi ne: Yara suna magana da karin kalmomin harshen waje, da sauraron karin waƙoƙin ƙetare, da ƙoƙarin kwaikwayon abubuwan da aka yi cikin bidiyo mai ban dariya na sauran ƙasashe, to, ko za su darajanta al’adun ƙabilar kansu? Shin suna kishin ƙasarsu?

Abu mafi baƙanta rai shi ne, yaran ba sa sani ba sun rasa wani abu mai matuƙar daraja. Saboda ba za a san abubuwa masu ban sha’awa cikin wasu al’adu, idan ba a fahimci harshe mai alaka da al’adun ba. Misali, cikin harshen Hausa, akwai wani karin magana wato “Da kaɗan-kaɗan matankaƙi ke shiga cikin gora”, maganar da ta kan iya sanya mutum tunanin ayarin matafiya: Wani matafiyi yana zaune yana hutawa a dab da wata rijiya, daga baya ya ga wani matankaɗi ya shiga cikin goransa. Ba a iya ganin kansa, sai dai wutsiyarsa dake bakin goran. Wannan abun ban sha’awa yana cikin wata gajeriyar jimla. Ban da wannan kuma, harshe na asali na iya ƙarfafa zumunci da haɗin gwiwa. Ba zan taba mantawa ba, lokacin da wani aboki na Bahaushe ya faɗa min “Ha!”, sai na buɗe baki kamar zan ce “Ah” amma ba tare da fitar da murya ba, abun da ya matuƙar burge shi, da sanya shi murna. Ya ce ya samu wani dan uwa a ƙasar Sin, saboda na iya Hausa, wato yarensa na asali.

Bari mu yi ƙoƙarin kare harshenmu na asali, kamar dai yadda ake ƙoƙarin kare lu’u-lu’un da ake gadonsu daga magabata. Don amfanin al’ummarmu da ƙasarmu, da kuma yaranmu.