Hasken haƙora

Daga AISHA ASAS

Haƙora na ɗaya daga cikin ɓangarorin jiki da ake amfani da su wurin fahimtar tsaftar mai su. Sau da yawa akan ƙyamace mutum ta sanadiyyar disashewar haoƙransa.

Da yawa an ɗora alhakin lalacewar hasken haƙora kan rashin tsaftace su.

Duk da cewa akwai ababen da ke iya zama silar ƙaurar hasken haƙora daga bakunan wasu, ma’ana, akwai na ƙazanta, sai dai akwai na ciwo ko na hallita.

Babban abin farin ciki ga masu matsalar rashin hasken haƙora shi ne, za su iya haskaka haƙoransu cikin sauƙi. Ta wacce hanya?

  1. Za ki iya amfani da bakin foda (baking powder) wurin haskaka haƙoranki, ta hanyar amfani da ita wurin goge baki, kamar dai yadda ake yi da buroshi. Wannan hanya ce mafi sauƙin ganin sakamako da za ki yi amfani da ita. Domin bakin foda na tattare da ababen da ke fatattakar ƙwayoyin cuta da kuma tabo mai wuyar fita kamar na haƙori. Amfani da ita a kowacce safiya zai iya zama silar haskaka haƙoran da suka yi duhu.
  2. Ta hanyar amfani da ‘hydrogen peroxide’ ma za ki iya haskaka haƙoranki. Sanannen abu ne ‘hydrogen peroxide’ na cire datti da korar ƙwayoyin cuta, sai dai a ɓangaren haƙora bayan wannan aiki, yana cire daɗaɗɗen tabon haƙora, ko dai na sanadiyyar tashin kulawa ko kuma wanda wani ciwon haƙora ya haifar. Kuma yana daga cikin aikin ‘hydrogen peroxide’ haskaka haƙora, ya kawar da duk wani duhu tattare da su.
  3. Shin ki na da masaniyar ‘ya’yan itace da kuma ganye da ake ci ba tare da dafawa ba na daga cikin hanyoyin haskaka haƙora ta hanyar yawaita cin su. Baƙin haƙora wanda mu ke kiransa da tsutsar haƙora, yakan tsaya ko da mun magance matsalar, wannan baƙin, ‘ya’yan itace da ganye na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke iya kawar da shi. Kuma yawan cin kayan marmari na taimakon haƙoran ta hanyar nisanta su da ƙwayoyin cuta da kuma kashe wasu daga cikin cututtukan haƙora waɗanda kan kai haƙoran ga disashewa.