Hassada ce ke kawo rashin jituwa tsakanin ƙungiyoyin marubuta – Momin Shukura

“Ina samun basirar rubutuna ne ta hanyar yin nazari kan abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummarmu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ƙungiyoyin marubuta adabin Hausa na kafafen sada zumunta da masu talifi suna da daman gaske, kuma kowacce ƙungiya da irin manufar ta, ko inda ta fuskanta wajen fitar da labaran da mambobin ta ke rubutawa. Duk da ƙalubalen da ake fuskanta wajen samun haɗin kan marubuta, musamman a ƙarƙashin ƙungiyoyi, da ƙananan damuwoyi irin na zaman tare, wata ƙungiya da ta zama gagarabadau kuma abin koyi ga wasu ƙungiyoyi ita ce Kungiyar marubuta ta Jarumai Writers Association, wacce ta zama ta farko daga cikin jerin ƙungiyoyin da aka kafa don yaƙi da labaran batsa. Shugabar ƙungiyar, Nana Basira Abubakar Musa wacce aka fi sani da Momin Shukura, daga Jihar Sakkwato ta bayyanawa wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu yadda ƙungiyar ta tsayu wajen ganin ta bambanta da sauran, wajen tsari da kuma samar da haɗin kan marubutan adabi.

BLUEPRINT MANHAJA: Zan so ki gabatar mana da kan ki.
MOMIN SHUKURA: Alhamdulillah. Sunana Nana Basira Abubakar Musa, ni marubuciya ce ‘yar asalin Jihar Sakkwato daga ƙarama Hukumar. Sai dai aure ya mayar da ni zama Asaba, babban birnin Jihar Delta a kudancin Nijeriya, inda nake zaune tare da iyalina. Ina kuma gudanar da ýan harkokina na kasuwanci irin na mata.

Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
To, ni dai tarihina ba wani mai yawa ba ne. Ni hafaffiyar Jihar Sakkwato ce, kamar yadda na faɗa a baya. Na yi makarantar Islamiyya kuma Alhamdulillahi na sauke Alƙur’ani Mai Girma, na yi karantun littattafai na addini da dama. Sannan kuma a ɓangaren boko na yi karatun firamare har zuwa sakandire, amma ban samu na shiga jami’a ba, aka yi min aure, kawo yanzu dai a nan karatuna ya tsaya. Ko da yake, da izinin Allah Ina son in cigaba da karatuna daga inda na tsaya. Tunda ita rayuwa kullum cikin neman ilimi ake yin ta.

Mai ya ja hankalinki ki ka fara rubutun labaran adabi?
Tunda farko ni ma’abociyar karatun littattafan Hausa ce sosai, na karanta littattafai masu yawa, daga nan ne na ji na fara sha’awar nima a ce na fara rubuta nawa littafin. Ko da yake da farko na ji alamun kamar ba zan iya ba amma ka san abin da mutum ya sa a ransa yana so. To, sai ga shi cikin yardar Allah kamar da wasa cikin lokaci ƙanƙani da fara rubutuna sai na ga abin na tafiya yadda na daɗe Ina sawwalawa a ƙwaƙwalwata.

Na fara da neman wata ƙawata da wannan magana kuma ba tare da wata matsala ba na samu goyon bayanta, ta taimaka min sosai wajen ganin burina ya cika, har lokacin da na fara rubuta littafina na farko ‘Na Ga Rayuwa’. Na ji tsoron cewa ba zan samu karɓuwa a matsayin sabuwar marubuciya ba, amma a haka na samu ƙarfin gwiwa sosai daga wajan ƙawayena da abokan arziƙi.

Alhamdulillah, a lakacin da na yi littafina na farko na samu cigaba, jama’a kuma sun yaba da ƙoƙarina sosai, na kuma haɗu da mutane iri daban daban, marubuta da waɗanda ba marubuta ba, sun bani gudunmuwa sosai da ba zan tava mantawa da su ba. Na haɗu da wata ƙawa wacce kuma ta zama min aminiya, ita ce ta riƙa ƙarfafa min gwiwa har na qara rubuta litatafi na biyu mai suna ‘Haɗuwar Zuciya’, a wannan lokaci na ga masoya sosai, kuma tun daga nan ne abin ya yi ta bunƙasa.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa?
E, gaskiya na rubuta littattafai guda huɗu, yayin da nake cigaba da rubuta wasu guda biyu. Littafina na farko shi ne ‘Na Ga Rayuwa’, sai ‘Haɗuwar Zuciya’, ‘Matsayi’ da ‘Matar Mahaifina Ce Sila’. Yanzu kuma Ina kan aiki kan ‘Ni Da Yaya Arifullah’ da kuma ‘Dakta Khairat’.

Ta wacce hanya ki ke samun basirar yin rubuce rubucen da ki ke yi?
Zan iya cewa shi rubutu baiwa ne da Allah Maɗaukaki Sarki yake bai wa mutane. Sannan ni Ina samun basirar rubutuna ne ta hanyar yin nazari kan abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummarmu, sai na yi tunani a kai kafin na fara rubuta labarin da nake so na yi.

Wanne tasiri ƙungiyoyin marubuta suke da shi, wajen taimaka wa ýan ƙungiyarsu?
Ƙungiyoyin marubuta suna ba da gudunmawa sosai, saboda suna ƙara ƙarfafa zumunci, domin a saboda ana zumunci a duk inda aka haɗu kan wata manufa. Ana samun haɗin kai, taimaka wa juna da shirya gasa ko tattaunawa a tsakanin ýan ƙungiya don a ƙara zaburar da juna, kan ayyukan ƙungiya.

A wacce ƙungiyar ki ke, kuma shin dama tuntuni a nan ki ke ko daga wata ki ka canza sheƙa?
First Class Writers Association ita ce ƙungiyar da na fara shiga kafin wani dalili ya sa na bar ta na koma Al’umma Writer’s Association wanda ita wani dalilin ya sa na fita. Yanzu kuma Ina Jarumai Writers Association wacce ni ce na kafa ta.

Kwanaki ƙungiyarku ta yi bukin cika shekaru biyu da kafuwa, Waɗanne nasarori za ku iya cewa kun samu kowa yanzu?
A shekaru biyu kacal da muka yi da kafa wannan ƙungiya, za mu iya cewa, mun samu nasarori ta hanyar rubuce rubucen mu, domin littattafan da muke fitarwa suna ɗauke ne da darussa masu muhimmanci da suka shafi zamantakewar al’umma, cigaban ƙasa, har ma da tsaro. Ba kawai darussan muke rubutu a kai ba, muna ma kuma samar da shawarwari na yadda za a samu zaman lafiya, haɗin kan ƙasa, da kyautatuwar tarbiyya da inganta zaman tare.

Bangon littafin ‘Na Ga Rayuwa’

A ɓangaren bukin cikar ƙungiyarmu shekaru biyu, mun shirya gasa tsakanin marubuta ba na ýan ƙungiyarmu ba kawai, wadda muka zaɓi muhimmin darasi kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaro a ƙasar nan, kuma marubuta da dama sun shiga har ma kuma an fitar da gwanaye daga ciki, su ne muka bai wa kyautar karramawa a taron da muka yi a Kano. Kuma muna shirye shiryen buga labaran waje guda don mu mayar da shi littafi, da za mu gabatar wa rundunar ýan sanda da gudunmawarmu, kan inganta tsaro a ƙasar nan.

Mai yake kawo rashin jituwa tsakanin ƙungiyoyin marubuta daban daban?
Hassada ce ke kawo rashin jituwar ƙungiyoyin marubuta. Sam wata ƙungiyar bata so ta ga wata tazarta ta duk da ba a taru an zama ɗaya ba. Basira da ɗaukaka Allah ne ke ba da ita. Ni Ina ganin idan muna haɗa kai muna zumunci a tsakanin mu, harkar rubutun adabi za ta cigaba sosai.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba.

Na gode.
Nima na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *