Hatsari da tashin bom a jirgin ƙasan Nijeriya

Daga ABDULWAHAB SULAIMAN

Sharhi a kan wannan batu da halin ko in kula na gwamnatin tarayya.

Ina mai fara wannan rubutu da jajanta wa iyalai da ‘yanuwa ga waɗanda suka rasa rayukansu a wannan iftila’i da ya shafe mu na garkuwa da jama’a ta hanyar sa bam a kan titin jirgin ƙasa. Kamar yadda kowa ya sani, mafi yawan al’umma ke amfani da wannan hanya wajen tafiya ne domin guje wa fitina da bala’in haɗuwa da masu garkuwa da mutane a kan hanya. Wannan al’amari na iya faruwa ga kowa.

Na tashi a yau ina mai tunanin, dama a ce ƙasata ƙasa ce mai cike da adalci ta kowanne fanni. Ina mai tunanin dama a ce wannan al’amari na garkuwa ta kafar jirgin ƙasa bai faru ba saboda shuwagabanni sun ɗauki darasi da kiyaye aukuwar wannan al’amari duba ga irin yadda aka yi ƙoƙarin cimma wannan al’amari a lokutan baya. Ina mai tunanin da ma ace gwamnatin tarayya ta ƙara matakan tsaro a hanyar babban titin Kaduna zuwa Abuja domin tsare rayukan al’umma kamar yadda titin yake a shekarun baya.

Ina mai nadama da aukuwar wannan al’amari duba da yadda waɗanda ke rike da kujerun mulki har kuka suka yi mana domin mu basu damar canza da kawo gyara cikin wannan ƙasar tamu kuma ga shi suna nuna mana halin ko in kula a kan wannan fitina da ke faruwa. Na so a ce wanɗanda suka yi muna alƙawarin kulawa da tsaro, cin hanci da rashawa, da haɓaka tattalin arzikin ƙasarmu suna iya cika alƙawarinsu. 

KARANTA: Harin jirgin ƙasa: ’Yan bindiga na barazanar kashe fansinjojin da suka sace

Da ma a ce Indiya ce ƙasarmu, inda ministan da ke kula da sufuri na jirgin asa ya yi murabus saboda jirgi ya faɗi bisa hanya. Manyan Hafsan Sojoji sun sauka daga muƙamansu saboda ‘yan ta’adda sun kai hari garin Mumbai a Indiya kuma sun ci nasara.

Amma a nan har kashe sojoji ake kamar kiyashi amma sai ko in kula daga manyan su. Ko da ma a ce ƙasa ta kamar Senegal inda ministan dake kula da sufuri ya sauka saboda jirgin ruwa ya kife da mutane da yawa. Na ce, dama a ce ƙasa ta na nan kamar Burkina faso in da shugaban ƙasa da dukkan Waɗanda ya saka cikin kabinet ɗinsa suka yi murabus daga kan kujerun su duba da sun kasa kare rayukan al’umma. Sai na dinga kawo misalai kamar yadda aka wayi gari aka samu shugaban ƙasa a ƙasar Norway da laifin hare-haren da ‘yan ƙunar baƙin wake suka kai wa ƙasar. Ko Babban birnin Belgium, watau Brussels In da ministan sufuri ya sauka da a ka kai hari a ƙasar.

Ina mai da ma a ce shugaban ƙasata wanda kundin tsarin mulkin ya ba shi umurnin tsare rayukan al’umma ya je har inda wannan iftila’i ya faru domin jajanta wa al’umma. Ba mu zaɓi Hafsosin Sojoji domin su zo su dinga bamu haƙuri ba. Ba haƙuri ke kare rayukan al’umma ba.

Mun wayi gari babu wanda ka iya fitowa ya ce laifin sa ne bisa ga irin waɗannan abubuwan dake faruwa kuma ga hanya mafita. Amma kowa ya ja bakin shi ya yi tsit kamar an tsikari kakkausa.  Ban so a ce ina ƙasar da iftila’i irin wannan ke aukuwa  amma ji kake ko’ina an yi shiru. Ya kamata a ce tun daga faruwar wannan al’amari ko ruwa kada a bari mugayen mutanen nan su sha ruwa.

Daga ƙarshe, ina mai miƙa buƙatarmu ga Shugaban ƙasar Nijeriya Janar Muhammad Buhari a kan:

Ka zo ma na da alƙawurra da dama kuma babu shugaban ƙasa da aka yi ma kyakkyawan amshi irin ka. Da ka yi ƙoƙari wajen magance dukkan matsalar tsaro a mataki na soja. Duk wanda ba zai iya ba, a kore shi a kawo wanda zai yi. Wannan ya shafi dukkan muƙamai da suka shafi tsaro. Kuma ka tashi tsaye kan dukkan ministocin ka domin kuwa mafi yawancinsu ba al’umma ba ne a gabansu.

Ƙari bisa bayani, ka sani cewa, talaka ya haƙura da samun ‘yanci a gwamnatinka. Abunda ya dame shi yanzu, ya samu ya yi noma ba tare da an kashe shi a cikin gonar sa ba. Ya samu abincin da zai ciyar da kansa da iyalansa ba sai ya je ya yi maula ko sata ba. Ko fannin ilimi abun ya haɗa a mataki na jihohi domin kuwa duk kanwar jance. An kai matsayin da ya’yan talakawa ba a ba su damar da za su iya cimma burin su a rayuwa. Ko me za a yi, ‘ya’yan masu hannu da shuni ake bawa.

Mun yi maka uzuri na ka gaji ƙasa da matsalolin tsaro, da matsin tattalin arzikin ƙasa. Amma a halin da ake ciki, hatta cikin birane ba a tsira ba. Gwamnoni sun kasa, saboda komai aka ce, sai a yi maganar cewa sai an ba da umurni daga gwamnatin tarayya.

Ina addu’ar Allah Ya zaɓa mana shuwagabanni na gari. Kuma ya sa da mu da shuwagabanni masu kishin cigaban al’umma, masu tausayin al’umma. Allah ka sa da mu da shugabannin da za su sa ido wajen tsayar da gaskiya da kwatanta adalci ba waɗanda za su faɗa cikin lissafin kuri da babakere kan dukiyar al’umma. Ya Allah ka kiyaye mu da kiyayewar ka. Allah ka ya ye mana wannan masifa, ka sada mu da zaman lafiya a ƙasarmu ta gado, Nijeriya. Ya Allah ka yafe mana zunubanmu, ameen ya Hayyu ya Ƙayyum.

Abdulwahab Sulaiman ya rubuto daga Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *