Hatsarin Neja: Hukumar kashe gobara ta ja kunnen direbobin tankar mai kan tuƙin ganganci

Daga USMAN KAROFI

Shugaban hukumar Klkashe gobara ta ƙasa (FFS), Injiniya Abdulganiyu O. Jaji, ya yi kira ga masu gidajen mai da direbobin tankokin mai su tsaurara matakan tsaro tare da guje wa tuƙin ganganci musamman a manyan hanyoyi da wuraren da ke da mummunan lanƙwasa. Wannan kiran ya biyo bayan mummunan fashewar tankar mai a Jihar Neja wanda ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutum 60 tare da jikkata wasu da dama.

Yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, Jaji ya nuna damuwarsa kan yawaitar fashewar tankokin mai da kuma tashin gobara a gidajen mai a ƙasar nan. Ya bayyana cewa akwai buƙatar duba tsare-tsaren da suka shafi jigilar mai tare da tabbatar da ɗaukar matakan kariya daga haɗari.

Jaji ya jaddada illar haɗarin tattara mai daga tankar da ta yi hatsari, inda ya ce wannan aikin yana da matuƙar haɗari ga rayukan jama’a. Ya ce, “ man fetur ko hayaki na iya kama wuta a kowane lokaci. Rayuwarku ta fi muhimmanci fiye da wasu ɗigo na mai.” Ya kuma yi kira ga al’umma su nisanci wuraren hatsari su kuma sanar da hukumar kashe gobara don ɗaukar matakan gaggawa.

A ƙarshe, Injiniya Jaji ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan haɗari tare da yaba wa jami’an agaji na farko kan irin jajircewarsu. Ya kuma yi kira da a hanzarta sabunta dokar hukumar kashe gobara ta 1963 da ke gaban majalisar ƙasa don kawo gyare-gyare da za su rage irin waɗannan munanan haɗura a nan gaba.