Hattara: ‘Yan damfara sun buɗe haramtattun  shafukan yanar gizo na E-Naira – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargaɗi al’ummar Najeriya a game da bullar wasu shafukan yanar gizo a kan E-Naira.  Wannan yana ƙunshe ne a cikin wani jawabi da Babban Bankin ya gabatar ranar Larabar da ta gabata. A cewar jawabin, tuni ma mazambatan suna can suna damfarar mutane.

Wannan aika-aikar ta biyo bayan ƙaddamar da sabuwar fasahar hada-hadar kuɗi ta E-Naira da aka gabatar da ita ga ‘yan ƙasar nan. Wadda shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya ƙaddamar da ita a ranar Larabar da ta gabata, 25, ga watan Oktoba, 2021.

A don haka, aka samu ɓullar shafukan zamba don cutar ‘yan Najeriya. A yanzu haka akwai wani shafin Tuwita @enaira_cbdc  wanda yake ikirarin daga CBN ɗin aka samar da shi. Wanda ko kusa ba ƙamshin gaskiya a cikinsa. Wannan ya tilasta wa Babban bankin kira da jan hankali ga ‘yan Najeriya da su kula su kasance a ankare.

Shi wannan shafi na Tuwita, @enaira_cbdc a halin ya yi nisa wajen jawo ra’ayin wasu ‘yan Nijeriya inda har yake kwaɗaita musu samun kuɗaɗe har Billion 50  na eNaira wanda ya yi ikirarin CBN tana rabawa. Inda har ya umarci mabiyansa da su shiga wasu adireshi na yanar gizo don buɗe asusu (wallet) domin su amfana da wancan tagomashi da ya yi ikirarin CBN ɗin za ta bayar. Abin mamaki, yanzu haka wasu masu tsautsayin sun faɗa tarkonsa har sun fara yi masa dafifi.

Saboda kawar da dukkan wasu shakku, shi ya sa CBN ya fito, ya barranta kansa da wancan shafin tuwita, (@enaira_cbdc). Sannan kuma ya ce sam ba mallakinsa ba ne. Kuma ba shi da alaƙa da shi. Sannnan kuma za a rufe shi a kan shafukan yanar gizo. 

Da wannan CBN ɗin yake gargaɗin ‘yan ƙasar nan da su guji duk wani shafi da yake ikirarin daga bankin yake. In dai ba waɗannan ba. www.facebook.com/myenaira; www.instagram.com/myenaira and www.youtube.com/myenaira ko a tuntuɓi lambar waya: 080069362472.

Daga ƙarshe, sun ƙaryata zancen cewa wai Bankin yana rabon wasu kuɗaɗe da aka ce tana rabawa. Don haka, sai mutane su yi taka-tsan-tsan don gudun faɗawa komar waɗancan ɓata-garin. Sannan kuma su yi rahotan duk wani abu da ya shafi hakan da ba su gamsu da shi ba.